Addini

Sautin Murya: Tsinanne Ne Kawai Ke Zagin Sahabban Annabi S.a.w~ Inji Khalifa Qaribullahi

Khalifan ‘Dariqar Qadiriyya na Afurka Dr Qaribullahi Nasiru Kabara ( Amirul Ansar) ya bayyana damuwarsa bisa dabi’ar cin zarafin sahabban Annabi da wani takadari ya dakko.
Malam Kabara ya ce” Ba ya daga d’abi’ar musulunci mutum ya mayar da rayuwarsa ta cin mutuncin mutane, yau a zagi wancan, gobe a zagi wancan, har ta kai ana kama sunan Sahabban Annabi S. a bayyane ba kunyar Allah ba yakana ana surfa musu ruwan ashariya, sayyadina Anasu shekara goma ya shafe ya na wa Annabi hidima, yadda Annabi ke son ‘ya’yansa haka ya ke son Sayyadina Anasu amma shi ake kama sunansa ana surfa masa ruwan ashariya, ko yaron gidanka ka ke wa haka kai Tsinanne ne ballanta sayyaduna Anasu bin malikin, ba wai masu zagin ne kad’ai tsinannu ba, hatta masu zama ana zagin suna jin dad’i suna ihu Billahil azeem la’ilaha illa huwa su ma tsinannu ne, kuma Allah ya tsine musu albarka”
Allah ya kara taimakon maulana Qaribullahi Khalifan musulunci, su kuma masu wannan aika-aika Allah ya shirye su idan su na da rabo.
Indabawa Aliyu Imam
Ga audion domin ku saukar kuji da kunnuwanku.
DOWNLOAD MP3Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button