Kannywood

Mun Fahimci Juna Sosai Da Iyayena Kafin Na Fara Sana’ar Fim– Jaruma Teema Yola

Advertisment

Tattaunawar WAKILINMU Tare Da JARUMA FATEEMA ISA Wadda A Ka Fi Sani Da Rukayya.
Da Farko Za Mu So Ki Fada Mana Cikakken Sunanki Da Kuma Takaitaccen Tarihinki.
To Asslamu alaikum warahmatullahi ni dai sunana Fatima, sunan mahaifina Isah, ni haifaffiyar Jihar Adamawa ce, an haife ni ne a garin Mubi. Na yi karatuna na Firamare da na Sakandire duka a Mubi. Sannan daga baya mu ka dawo Jimeta da iyayena gaba daya mu ke zaune. Wannan shi ne takaitaccen tarihina.

Jaruma Teema
Daga Sakandire Ba Ki Ci-gaba Da Karatu Ba Kenan?
Eh gaskiya ban ci-gaba ba, na so dai na ga na dora amma abun bai yiwu ba, kasan ba a tauna taura biyu a lokaci daya. Idan karatun, to karatun, idan kuma aiki to aiki. To amma har yanzu kokarin da na ke yi kenan na ganin na koma makaranta.
To Fatima Me Ya Ja Hankalinki Ki Ka Fara Wasan Hausa?
To kasan kowa da irin abunda ya ke shigo da shi wanann masana’anta, wani za ka ga ko rashi ne ya ke kawo shi idan ya zo kuma sai ya dauke shi sana’a. To amma ni gaskiya tun ina karama ina da sha’awar harkar fim, mun tashi mu na kallo a gidanmu, su na ba ni sha’awa, to kuma gashi yanzu Allah Ya cika min burina. To gaskiya dai ni kishin harshena da addinina ne ya sa ka ni shigowa fim, kuma na dauke fim a matsayin sana’a. Yadda kowa ya ke daukar sana’arshi da muhimmanci haka ni ma na ke daukar fim. Saboda ina samun ci da sha da kuma sutura a cikin sana’ar fim. Saboda irin tasirin da fim ya ke da shi da kuma sakon da ya ke aikawa. Kasan wasu ba sa sauraran rediyo, to tasirin fina-finai ya kan sa a isar da muhimmin sako ta hanyar.

Wane Irin kalubale Ki Ka Fuskanta Musamman Daga Gida A Lokacin Da Ki Ka Nuna Sha’awar Shiga Harkar Fim?
Gaskiya ni dai ban fuskanci wani kalubalen ba, saboda ina da kyakkyawar alaka da iyayena. Saboda nasan duk abinda su ka ga zai zama matsala agareni ba za su bar ni in yi ba. Kuma da ya ke sun fuskance ni ban samu wani kalubale ba, akodayaushe fatan alkhairi ne a tsakaninmu.
To Daga Wajen Al’umma Fa Wane Irin kalubale Ki Ka Fuskanta?
Eh to kasan shi dan Adam ajizi ne, kowa da irin yadda tasa ta ke zuwar masa. To dole wani zai ganka ya ji ya na kaunar ka wani kuma ya ganka ya ji ba ya kaunar ka. Wani kuma zai ji ya na yi wa harkar wata iriyar fahimta. To idan ba wanda ya ke kusa da kai ba ya zauna da kai ba kowa ne zai fahimci yadda harkar ta ke ba. To shiyasa za ka ga mutane daga gefe wasu su na kalubalantarku su na fadar wasu maganganu a kanku, to dole sai dai ka toshe kunnanka tunda kai ba abunda ya kawo ka ba kenan.
To A Cikin Masana’antar Fa Wanne Irin kalubale Ki Ka Fara Fuskanta Lokacin Da Ki Ka Shigo?
To gaskiya ni dai na shigo da kafar
dama.
Au Daman A Na Shigowa Da kafar Hagu?
Hhhh Eh a na shigowa da kafar hagu mana.
To Ta Ya Ya A Ke Shigowa Da kafar Hagu?
To ai wasu za ga ji su na cewa sun sha wahala farkon shigowa. Amma ni dai ban samu wannan kalubalen ba, na fado a hannu na gari hannun mutane masu sanin darajar Dan Adam. Sannan su na kokarin duk wani abu na alkhairi su ga sun saka ka a ciki, to ka ga ni ban samu wannan kalubalen ba. Sannan kuma abokan aiki mu na zaune da kowa lafiya. Za a yi wasa faran-faran da kowa, kasan ance sana’a mai hada zumunci. Ta hada ka da wannan ta hada ka da wanchan.
A Cikin Tarin Fina-finanki Wanne Ne Fim dinki Na Farko Da Ki Ka Fara Yi?
To ni dai fim din da a ka fara saka min (Camera) shi ne fim din “Dakin Amarya”. Na fito ne a matsayin ko kanwar Atete ne ko kanwar Tsamiya na dai manta gaskiya.
To Izuwa Yanzu Za Ki Iya Fada Mana Adadin Fina-finan Da Ki Ka Yi?
Toooo gaskiya ban san adadin fina-finai ba.
To A Cikin Fina-finan Da Ki Ka Yi Wanne Fim Ne Ya Fi Burge Ki Wanda Kodayaushe Ki Ke Tuna irin Rawar Da Ki Ka Taka A Ciki?
Fina-finaina da na ke so kuma na ke alfahari da su su na da yawa gaskiya. Amma tabbas ina matukar ji da shirin “Labarina” ina mugun jin sa, har cikin raina na ke jin shi saboda irin rawar da na taka a wannan shirin Allah Ya yi yawa da shi. To gaskiya ba wanda na ke jin a zuciyata kamar “Labarina”.
To Mu Dawo Cikin Shi Wannan Shiri Na Labarina Kashi Na 9 Na Daga Cikin Inda Ki Ka Taka Muhimmiyar Rawa A Cikinsa Me Za Ki Iya Cewa Game Da Wannan Fitowar?
To gaskiya shirin Labarina kashi na 9 sai dai godiyar Allah, saboda ya wuce tunanin mai tunani. Duk yadda na ke tunaninsa ya wuce haka. Saboda na samu kulawa sosai-sosai daga wajen masoya a sanadin wannan kashi na 9. Na samu kulawa daga wajen mutane bila’adadin. Tun daga wannan makon har yau, ko yanzu idan na bude wayata za ka sakon Labarina. Ko’ina Labarina, Labarina, to sai dai mu ce sai dai godiyar Allah.
Wasu Na Ganin Cewa Kamar Ku Na Da Wata Alaka Ta Musamman Da Jaruma Nafisa Abdullahi Tun Kafun Haduwarku a Shirin Labarina Me Ne Ne Gaskiyar Wannan Magana?
Gaskiya babu alaka ta kusa sosai tsakanina da Nafisa, sai dai akwai girmama juna a tsakaninmu. Har kuma mu ka zo mu ka hadu a cikin shirin Labarina.
A Lokacin Da Ku Ke Daukar Wannan Shiri Da Ku Ka Zo Daukar Wajen Da Ki Ke Fadawa Mahmud Wannan Maganganu Masu Zafi, Ba Ki Ji Kamar A Gaske Ne Ki Ke Fada Masa Wannan Zafafan Maganganu Ba?
Aa ni fa sam ban ji ba, saboda idan ka kalli shirin za ka ga abunda ya dace da Mahmud kenan ai. Saboda duk wanda ya kalli shirin zai ga cewa, wata iriyar soyayya Mahmud su ke da Sumayya. Tun ta na burge ka har sai ta koma ta na baka haushi. Saboda shi Mahmud wani irin mutum ne, mai zafin kishi da Kuma jiji da kai, samsam bai iya kula da mace ba, to ta ya abokin hamayyarsa ba zai kwace masa mace ba. To abin da zafi dai gaskiya kuma kowa zai gan shi da zafi.
A Cikin Jarumai Maza Na Wannan Masana’anta Wanne Jarumi Ne Ya Fi Burge Ki?
Ehh to gaskiya ina yin Nuhu Abdullahi sosai, amma kafun na shigo masana’antar fina-finai ina matukar yin Sadeek Sani Sadeek.
A Jarumai Mata Fa?
A mata ina son (acting) din Rahama Hassan da kuma Jamila Nagudu. Idan za ka lura da zafin (acting) dina za ka ga irin na Rahama Hassan ne.
Me Ne Ne Babban Burinki A Rayuwa Yanzu?
Gaskiya babban burina yanzu shi ne na yi aure. Ba ni da wani buri da ya wuce na yi aure gaskiyar magana kenan. Saboda rayuwar mace kalilan ce, idan Allah Ya ba ka dama to ka yi amfani da shi a iya lokacin, idan ya wuce ba lallai ya dawo ba sai dai ka ji wasu su na yi.
A bangaren Abinci Wanne Abinci Ki Ka Fi So?
To a bangaren abinci gaskiya na fi son wake da shinkafa da mai da yaji.
A bangaren Kaloli Fa Wacce Kala Ki Ka Fi So?
Eh a bangaren kaloli na fi son (Black and White) da kuma (Pink) su ne kalollin da na fi so.
Wanne Sako Gareki Zuwa Ga Masoyanki Masu Kallon Fina-finanki Musamman Shirin Labarina?
To Alhamdulillah ina ta burin na samu damar godewa masoyana daman, ina godiya sosai a gare su.leadershipayau na ruwaito.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button