Labarai
Mujallar Charlie Hebdo ta sake yi wa Manzon Allah Annabi Muhammadu (SAW) ɓatanci
Lamarin na zuwa ne kwana ɗaya kafin soma shari’ar mutanen da suka kai hari a ofishin mujallar
Mujallar nan ta ƙasar Faransa Charlie Hebdo wadda ta shahara wurin zanen barkwanci ta sake wallafa wani zane na barkwanci inda suka siffanta Annabi Muhammad S.A.W.
Irin wannan katoɓarar da mujallar ta yi a 2015 ne ya sa aka kai mata hari a shekarar 2015.
Sake wallafa zanen na zuwa ne kwana ɗaya kafin soma shari’ar mutanen nan 14 da ake zargi da taimaka wa wasu mutum biyu masu iƙirarin jihadi da kai harin bindiga a ofishin mujallar a ranar 7 ga watan Janairun 2015.
An kashe mutum 12, ciki har da wani shahararrun masu zanen barkwanci. An sake kashe wasu mutum biyar a wani hari na daban a birnin Paris kwanaki biyar bayan harin farkon.
Waɗannan hare-haren su ne mafarar kai hare-haren masu ikirarin jihadi a fadin Faransa.
Shafin farko na mujallar na ɗauke da zanen barkwanci har guda 12 na Annabi Muhammad S.A.W, waɗanda aka wallafa a wata jaridar harshen Danish kafin aka wallafa su a mujallar Charlie Hebdo.
Ɗaya daga cikin zanen barkwancin ya nuna Annabi Muhammad S.A.W sanye da bam a kansa a maimakon rawani.
A sharhin da ta wallafa, mujallar ta ce tun abin da ya faru a 2015 ake yin kira a gare ta da ta ci gaba da zane-zanen barkwanci.
“A kullum mun ƙi yin hakan, ba wai don za a hana ba – doka ta ba mu damar mu yi hakan – amma muna buƙatar hujja mai kwari don mu yi hakan, hujja wadda ke da ma’ana kuma wadda za ta kawo wani abu na muhawara,” in ji mujallar.
Ta kara da cewa: “Sake wallafa irin wannan zanen a makon da ake yin shari’ar waɗanda suka kai hare-haren 2015 abu ne mai muhimmanci a gare mu.”bbchausa.com na ruwaito
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com