Labarai
KHADIMUL UMMAH : Babagana Zulum Ya ‘Yanto Garin Baga Daga Hannun Boko Haram A Yau (Hotuna)
Tsarki ya tabbata ga Allah, Maigirma gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum (Khadimul Ummah) ya bude garin Baga a karo na farko a yau asabar domin dawo da mutane ‘yan gudun hijira
Gwamnan ya duba ayyukan da akayi na gyaran gurare masu muhimmanci a garin Baga, kama daga Asibitoci, ruwan fanfo, makarantu, masallatai da sauransu
A jawabin da gwamnan yayi, yace barazanan harin ta’addanci a kansa ba zai canza masa ra’ayi na ganin karshen bayan ta’addancin Boko Haram ba
Yaa Allah Ka kareshi, Ka cika masa burinsa na ganin karshen bayan ta’addancin Boko Haram da masu tallafa musu Amin.
Ga hotunan nan.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com