Labarai

Jarumin Da Ya Fito A Matsayin Zazzaky A Fim Din “Fatal Arrogance” Yace An Fara Barazar Kashe ni ~Edochie

Kungiyar ‘yan uwa Musulmai mabiya akidar Shi’a (IMN) sun fara kaiwa Pete Edochie, jarumin masana’antar Nollywood farmaki 

 – A cikin wani fim da Anosike Kingsley Orji ya dauki nauyi, an nuno Pete Edochie ya fito a matsayin Zakzaky 

 – Kungiyar IMN sun fara kai masa harin ne saboda fitowarsa a matsayin El-Zakzaky a cikin fim din

Kungiyar IMN sunce suna zargin hukumar sojin Najeriya da daukar nauyin fim din nan mai suna “Fatal Arrogance” saboda suyi kokarin rufe laifinsu na kisan wulakancin da suka yiwa ‘yan Shi’a 348 a watan Disambar shekarar 2015.

Haka kuma kungiyar ta caccaki Pate Edochie sakamakon fitowa a matsayin El-Zakzaky a cikin sabon fim din. Inda jarumin da bakinsa yace ana farautar rayuwarsa.

A wata hira da Sahara Reporters sukayi da Edochie yace: “Ban fahimci dalilin ‘yan Shi’a na kai min farmaki ba, akan fim din da ko fita beyi ba. Domin yanzu haka ba’a gama tsarashi ba ma.”

Ya kara da cewa “da zasu kai kara ga sifeto janar na ‘yan sanda, yace a kawo fim din yagani, bansan ya zamuyi dasu ba saboda babu fim din ma a kasa.”

“Bai kamata inyi kwaikwayon shugabansu ba ko kuma yin isgili a gareshi” a cewar shi.

Ina shawartarku da ku ajiye makamanku, ku kuma kara hakuri har a saki fim din. Idan kunga abinda kuke zargi, sai kukai kukanku ga Sifeto janar na ‘yan sanda.

“Ko menene kukeyi yanzu bai dace ba, a cewar Edochie. “Indai akan wannan fim dinne, zanso ku dakata har sai an ‘karasa shirya fim din.”

Ya kara da cewa “bani na rubuta fim dinnan ba, kuma Kingsley Orji Anosike shine ya dauki nauyin fim dinnan. Kuma idan kunaso ku kai ‘korafinku akan fim din, sai ku jira ku kalla, alabarshi sai ku nuna takaicinku ga wanda ya dauki nauyin shi, amma bani ba wanda a jarumi kadai na fito a fim din. Nifa babu ruwana.

Ya kuma mika godiyarsa inda yake cewa “Nagode ma duk wadanda suka sanar dani ‘kokarin kai min farmaki da ‘yan Shi’a suke yi, ina godiya ‘kwarai. Nifa cikakken Dan Najeriya ne mai cikakken ‘yanci. Babu inda zan gudu, saboda hakan wasu zasu so.”

‘Kungiyar ‘yan Shi’a sun mayar da martani ga Pete Edochie inda suke cewa yayi babbar wauta da aka yi amfani dashi wajen daukar wannan fim, sannan suka karyata zargin da yake na cewa an kai mishi hari

Mai magana da yawun ‘Kungiyar, Ibrahim Musa yace “jarumin ya taka rawar da ke nuna munin Shi’a a idon duniya. Kungiyar sunce bayanan Edochie shirmene da kame-kame.

“Koken da ‘kungiyar IMN ta bayyanar a gaban Sifeta janar na ‘yan sanda da kuma ‘kungiyar shirya fim bata nuna kai farmaki ga rayuwar kowa ba. Tsoratarwa bata daya daga cikin halayyarmu” a cewarsa.

“Idan da Edochie yana da wata halayyar ‘kwarai kamar yanda yake ikirari,da bai amince da fitowa ba yana bata sunan wanda aka zalinta irin Sheikh El-zakzaky a idon duniya ba, kuma har yayi tunanin bai yi wani laifi ba.

Duk wani jarumi da ya amsa sunansa, yakamata ya dinga bin tsarin labari daki-daki kafin ya amince ya fito a fim din da akayi mishi tayi.

Da kuma ace yabi labarin tsaf da zai gane cewa anyi fim dinne musamman saboda abinda ya faru a Zaria a 2015 wanda hakan ya jawo asarar rayuka da dama, da zai fahimci irin cin zarafi da kisan wulakanci da akayi wa mutane da kuma rufe gawawwakin su a matsayin ganganci.

Tabbas da ya fahimci cewa har yanzu ICC suna bincike akan lamarin. Kuma wannan labarin dake gabanshi cigaba ne na ‘kara boye gaskiya.

Tuni ‘Kungiyar Shi’a ta gabatar da korafinta na game da fim din ga Sifeto janar na ‘yan sanda.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button