Kannywood

Jarumi Hamisu Iyatama Yayi kira Da Babbar Murya Ga shugaban ƙasa Akan Halin Da Al’umma suke ciki

Advertisment

Jarumi hamisu yan tama yana daga daga cikin jaruman fina finai da na goyawa buhari baya tun daga shekara 2015 har i zuwa 2019 wajen kamfanin na a zabe shi.
Shine ya wallafa wannan kira ga shugaban kasa da kuma sauran shuwagabannin akan irin yadda ake ciki da su bi al’umma irin halin rayuwa da ake ciki.
Ga jawabin da ya wallafa a shafin na facebook.
Tafiya yajin aiki?
Yan Nigeria na cikin wani hali da yanayi na rashin jin dadin rayuwa da walwala”

Da farko dai…

Covid19 tazo tayi babbar illa ga tattalin arzikin kasa da Yan,kasa.
Gwamnatin tarayya tazo tayi karin kudin haraji ga dukkan abun dan Nigeria zai siya sai anciri 7.5% daga me sayan kayan masarufi kai  komai ma.

Ga karin kudin kudin wutar lantarki mai yawan gaske dadin dadawa kuma ko nawa kabiya kudin wutar sai an cire VAT na kaso 7.5% daga cikin kudin daka bayar. Misali idan kaje sayen wutar dubu 5 toh wutar 4651.1 za a baka an cire naira 348. 84 a mtasayin vat wannan chaji ne ga masu 3 phase meter.duk unit daya zai kama akan naira 48.09 sabanin da Naira 29 da wasu yan dakika.
Ga karin kudin Petrol,duk lokacin da aka kara kudin Mai toh duk kayan masarufi da zirga zirga jama,a sai sun samu kari ta kowanne fanni.

Ga Sana’oin jama,a duk sunja da baya,da yawan al,ummar kasa basa samun riba asana,oin su kamar shekarun baya.wasu ma karyar da kayan sukeyi su fadi kasa wanwar don su samu suyi wa iyali cefane.
Ga tashin gwaron zabi da Dollar tayi duk da cewa ta dan sauka amma farashin abubuwa basu chanja kamar yadda ake zato ba.
Gashi da yawan ma,aikata na Gwammnati basa zuwa aiki kuma wasu an zaftare musu albashi.
Ga mamoman mu sun tafka babbar asara musanman manoman shin kafa a yobe da kebbi da Jigawa da wasu sassa ruwan sama yayi musu ta,adi sosai.
Ga Yan kasuwa matafiya basa fita kasashe domin saye da sayarwa haja,saboda jirage basa zirga zirga.

Kamfanonin cikin kasa a durkushe saboda karancin wutar lantarki da tsadar desel da hau hauhawar Dolars wato Forex.
Ga Makarantu a rufe tun daga jami,a har Nursery hannun agogo ya koma baya.

Advertisment
Ba,asan ta ina za,a fara ba kuma yaushe za,a koma gaba daya.

Ga Ga Ga Ga din tayi yawa.
Yanzu kuma za,a shiga yajin aikin na kungiyoyin kwadago na kasa baki daya domin nemawa al,ummar kasa sauki
ko Gwammnati mai karfin iko zata saurare su taji kan mu baki daya…?

Idan har gwammnati taki rage wadannan kare karen kudade da tayi akan yan kasarta toh yajin aiki zai kan kama kunga mun kara tsunduma cikin wata musiba da bawanda yasan me zata kara haifarwa da tattalin arzikin kasa da na al,umma

kasa.

Waiyo kasata Nigeria da Yan kasata baki daya Allah ya bamu sauki cikin rayuwannan.
Gaskiya muna cikin tsaka mai wuya sosai matuka gaya kawai dai ta ciki na ciki kowa ka gani a fuska sai murmushi da wasa da dariya da fara,a amma cikin zuciyar akwai kuna mai zafi da raradi.
Kowa ka gani musanmam anan arewa  sai karfin hali da tawakkalin cewa komai kagani daga Allah ne.

Da yawan  Jama,ar mu sai sayar da kadarori suke tayi wato tsohuwar ajiya domin aci a rayu.

Kalilan ne cikin miliyoyin Yan kasa ke warwasawa saboda lokacin sune yanzu.

Don Allah Shugabannin Kasata Nigeria da wakilan mu birnin tarayya da jiha kuyi karatun ta nutsu ku taimakawa al,umnar kasar nan domin ganin Yan Nigeria sun samu saukin rayuwa.

Kar ku bari yajin aikin da akeso a fara ranar litinin ya kankama. Shugabanni
ku tuna Shi shugabanci dan al,umma ake yinsa kuma tare da al,umma akeyin sa kuma dole al,ummar ake mulka saboda haka bamuji dadin wannan karin haraji da wuta da petrol da akayi ba.idan da ace duniya zaune ake cikin kwanciyar hankali harkoki na gudana kamar yadda ya kamata don kunyi kari baza mu damu ba wallahi.


Shugaba Muhammadu Buhari a tausaya mana a rage karin da akayi mana kan wutar lantarki da Nau,in Mai.
Alummar kasa sun zabe ka domin su samu chanji da jin dadin rayuwa kuma suna sonka har gobe.A tausaya! A sassauta! A tallafa ! Rayuwar  yan kasa  su samu sauki.
#Iyantama”

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button