Kannywood

Jarumar Kannywood na matuƙar kwantar min da hankali – Femi Fani-Kayode

Tsohon ministan zirga-zirgar jiragen sama na Najeriya Femi Fani Kayode ya ce jarumar Kannywood Halima Yusuf na matuƙar kwantar masa da hankali.

Ya kuma musanta cewa zai saki matarsa kana ya auri ita jarumar da cewa duka jita-jita ce maras tushe.

Mr Fani-Kayode ya kuma ce jarumar wacce ake ta rade-radin matar da zan aura ce “aminiyata ce wacce nake matuƙar mutuntawa da ganin ƙimar ta.”

Kauce wa Instagram, 1

Karshen labarin da aka sa a Instagram, 1

“Ana yada jita-jita a shafukan sada zumunta cewa ina shirin sake sakar matata. Hakan ƙarya ne. Miss Halima Yusuf, wacce aka ce budurwata ce, ƙawata ce kuma makusanciyata wacce nake matuƙar girmamawa,” in ji shi.

BBCHAUSA ta ruwaito cewa ya kara da cewa: “Ita da wasu irinta, sun kasance cikin mutanen da suke matuƙar kwantar mini da hankali kuma ina matuƙar godiya a gare ta.”

Tsohon ministan ya buƙaci mutanen da ke watsa jitar-jita kan batun su daina.

Wannan layi ne

Yawan jawo ce-ce-ku-ce

Kauce wa Instagram, 2

Karshen labarin da aka sa a Instagram, 2

Femi Fani-Kayode mutum ne mai yawan yawo ce-ce-ku-ce a kafafen watsa labarai, inda na baya bayan nan ma sai da ya tayar da ƙura bayan da ya ci zarafin wani ɗan jaridar Daily Trust a Najeriya.

A cikin watan Agustan wannan shekarar ne dai wani faifen bidiyo da ya mamaye shafukan sada zumunta ya nuna tsohon ministan yana ta zagin ɗan jaridar, Eyo Charles.

Dan jaridar dai ya yi masa wata tambaya da ya yi masa da ba ta yi masa daɗi ba, a lokacin wata hira da ‘yan jarida a birnin Calaba na Jihar Cross Rivers da ke Kudancin Najeriyariya

Amma daga bisani ya fito ya nemi afuwa bayan da wasu ‘yan Najeriya, ƙungiyoyin kare hakkin ‘yan jaridar da na bil adama har ma da kafafen watsa labarai na cikin gida da na ƙasashen waje suka yi masa rubdugu.

Har ila yau a watan Yulin shekarar nan ma sai da sarautar gargajiyar da Sarkin Shinkafi Alhaji Mumammadu Makwashe ya bai wa tsohon ministan ta tayar da ƙura.

Sarautar “Sadaukin Shinkafi” da masarautar Shinkafin ta ba shi ta janyo ce-ce-ku-ce a ciki da wajen masarautar, inda wasu daga cikin masu riƙe da muƙaman gargajiya suka ajiye muƙaman nasu.

BBCHAUSA ta kara da cewa Femi Fani-Kayode dai ya shahara wajen yin kakkausar suka ga duk abin da ya shafi arewacin Najeriya da kuma Hausawa.

Kalamansa kan kabilun Hausawa da Fulani sun sha tayar da ƙura a ƙasar musamman ma a shafukan sada zumunta.







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button