Uncategorized

innalillahi wa innaa ilaihi raji’unn ! Boko Haram Aun Kaddamar Da mummunan Hari Ga Tawagar Gwaman borno Zulum

Yau juma’a ‘yan ta’addan Boko Haram sun kaddamar da mummunan harin kwanton bauna wa tawagar Maigirma gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum

Tun jiya tawagar gwamnan ta bar birnin Maiduguri zuwa Monguno, ana shirin kwashe ‘yan gudun hijira mutum dubu daya daga garin Monguno zuwa asalin garinsu na Baga

Datti Assalafy ya kara da cewa jami’an tsaron sun fara yin gaba daga garin Monguno zuwa Baga, sun iso daidai wani kauye da ake kira Korochara kusa da sansanin sojojin hadin gwiwa na kasashen dake iyaka da tafkin Chadi, wato Multi National Joint Task Force (MN/JTF), sai Boko Haram suka kaddamar musu da harin kwanton bauna

‘Yan ta’addan sun kashe ‘yan sanda guda 8, sojoji guda 3 da ‘yan kato da gora Civilian  JTF guda 4, sai kuma wadanda suka samu munanan raunuka

Datti Assalafy ya kara da cewa, bincike ya nuna mana cewa zolayar kaine ace za’a mayar da mutane garin Baga a halin yanzu, saboda sunnar Boko Haram ne idan bakaje inda suke ba to su zasu zo inda kake, saboda kaf zagayen kasar garin Baga babu inda zaka fita ya kai nisan kilomita 8 baka hadu da Boko Haram ba

Babu su a cikin garin Baga, amma suna gewaye da garin, don haka ya kamata gwamnatin jihar Borno da na tarayya su sake shiri da daukar matakin da ya dace

Allah Ya sauwake, Ya kawo mana karshen wannan masifa Amin

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button