Labarai
INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN: Sarkin Biu Dake Jihar Borno Ya Rasu
Allah ya yi wa Sarkin Biu dake Jihar Borno, Mai Martaba, Alhaji Mai Umar Mustapha rasuwa.
Iyalansa sun tabbatar da rasuwar sa. Ya rasu yana da shekaru 79. A shekarar 1989 ne Marigayin ya zama Sarki.
Allah ya jikansa da rahma, ya gafarta masa, Allah ya kwautata makwancin sa. Amin.
Daga Babangida A. Maina
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com