Kannywood
Hamisu Breaker: Waƙar Jarumar Mata ce ta 6 da aka fi kallo a Youtube a Najeriya
Advertisment
Shafin TurnTable Charts na Tuwita ne ya fitar da jadawalin waƙoƙi 10 da aka fi kalla a YouTube a Najeriya a makon da ya gabata, inda aka kalli Jarumar Mata sau 74,900 cikin mako ɗaya kacal.
Ga jerin waƙoƙin kamar haka:
- Cardi B & Megan Thee Stallion – WAP; 393k
- Simi – Duduke; 86.2k
- Laycon – Fierce (ft. Reminisce & Chinko Ekun; 84.9k
- 2Baba ft. Wizkid – Opo; 84.8k
- Dj Tunez ft. Wizkid – Cool Me Down;
- Hamisu Breaker – Jaruma; 74.9k
- Omah Lay – Lo Lo; 71.1k
- Beyonce, Shatta Wale & Major Lazer – ALREADY; 68.4k
- Fireboy DML – Tattoo; 62.1k
- Peruzzi – Lagbaja; 60.2k
bbchausa na wallafa,wakar Jarumar Mata dai na ci gaba da jan zarenta a Najeriya saboda irin ɗumbin farin jini da ta yi tun bayan gasar rawarta da wasu matan auren suka yi.
Hamisu Breaker ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa, “Sai godiya,” yana mai nuna farin cikinsa kan wannan nasara da waƙarsa ta samu.
Su ma wasu ƴan masana’antar Kannywood suka taya shi murna a shafukan sada zumuntarsu.
Advertisment
Ali Nuhu ya ce: ”Ina taya ka murnar Hamisu Breaker Ɗorayi, wannan babbar nasara ce.”
Waƙar Hamisu Breaker ce kawai ta Hausa da ta shiga wannan jeri na guda 10 da aka fi kallo a YouTube a makon da ya gabata, kuma mafi yawan waɗanda suka kalle ta daga arewacin ƙasar ne.
Waiwaye
Tun bayan da bidiyon gasar rawar matan aure ya zama ruwan dare gama duniya a arewacin Najeriya da aka yi lokacin bikin sallah, sai hankalin mutane ya koma kan wakar da ta sa suka taka rawar.
Wannan waka dai takenta shi ne ‘Jarumar Mata’wadda Hamisu Breaker Dorayi ya rera.
Duk da cewa mawakin ya ce ya yi wakar ne a karshen shekarar 2019, kuma ya sake ta a farkon 2020, za a iya cewa dubban mutane ba su san ta ba sai a makon bikin karamar sallah, bayan da wasu matan aure suka yi yayin yin rawarta.
A wata hirar bidiyo kai tsaye da BBC Hausa ta yi da Hamisu Breaker a shafinta na Instagram, matashin mawakin ya ce wannan gasa da mata suka yi ba karamin farin jini ta kara masa shi da wakar ba.
Ya ce: ”Wakar ta yi matukar tashe a lokacin da ta fito amma na yi tunanin ma tashenta ya dan ja baya, kawai kwanan nan sai na ji ta sake karade duniya.”
‘Abin da ya sa na yi wakar’
Breaker ya ce bai san adadin mutanen da suka kira shi a waya don sanar da shi cewa ya ga yadda wakarsa ta yi tashe a wannan dan tsakanin na bikin sallah ba.
BBC ta tambaye shi kan ra’ayinsa kan rawar matan aure a bidiyo a saka a shafukan sada zumunta.
Sai ya ce duk da dai a tunaninsa sanya rawar a social media din na iya zama kuskure. Amma tun da ni ba malamin addini ba ne ba zan iya fashin baki kan hakan ba.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com