Labarai

Gwamna Matawalle ya buƙaci mai tattaki daga Kaduna zuwa Zamfara ya koma inda ya fito

Gwamna Bello Matawalle ya nemi matashin nan da yake tattaki daga wani yanki na jihar Kaduna zuwa Zamfara da ya koma inda ya fito.

Gwamnan ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.

Bbchausa na ruwaito daga shafin twitter, gwamnan dai ya shawarci matashin ya nemi wani abu mai muhimmanci ya yi a maimakon jefa kansa cikin kasada.

A cewar gwamnan, “a matsayina na uba, ina son na hana matasa jefa rayuwarsu cikin haɗari, a don haka nake fatan zai dakatar da tatakin tare da mayar da hankali kan wani abu da zai amfane shi.”

Wannan ba shi ne karo na farko da matasa ke yin tattaki ba ga shugabanninsu, inda ko a 2015 ma sai da wani matashi ya kwatanta yin haka bayan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ci zaɓe.

I appreciate the solidarity of the courageous youngman said to have embark on long trek to honour me.
As a father, I want to discourage young people from such dangerous adventures, I sincerely hope he discontinue the trek and channel his energy into a more productive activity.

— Dr. Bello Matawalle (@Bellomatawalle1) September 25, 2020

Hakazalika an samu wani matashin ma da ya yi tattakin zuwa Kano tun daga Katsina domin taya gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje murnar lashe zaɓe a 2019.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button