Labarai

Gwamna El-Rufai ya bada Hutun kwana ukku zaman makoki saboda mutuwar Sarkin Zazzau

Advertisment

Gwamna Nasir El-Rufai ya fitar da ranakun makokin Sarkin Zazzau

Babu wanda zai fita aiki Ranar Laraba saboda wannan rashi da aka yi
Alhaji Shehu Idris ya rasu ne a babban asibitin Soji na 44 a Kaduna jiya

Gwamnatin Nasir El-Rufai ta bada ranakun makoki a fadin jihar a sanadiyyar mutuwar Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris.

Za ayi kwanaki uku a jere ana makokin Marigayin kamar yadda gwamna ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a ranar 20 watan Satumba.

Advertisment

jaridar Legit ta kara da cewa ,al’umma za su yi amfani da wannan dama domin yin addu’o’i da karbar gaisuwar makokin wannan babban rashi da aka yi a jihar Kaduna.

Mai taimakawa gwamnan Kaduna wajen yada labarai, Mista Muyiwa Adekeye, ya ce ba za a rika fito da tutoci sama a wadannan ranaku uku ba.

Marigayi Sarkin Zazzau, Shehu Idris
Za a shiga wadannan ranakun makoki ne daga Litinin 21 ga watan Satumba zuwa Laraba, 23 ga wata, inji hadimin mai girma gwamnan Kaduna.

A ranakunan Litinin da kuma Talata za a zo aiki a ofisoshin gwamnati kamar yadda aka saba, amma ranar Laraba babu wanda zai yi aiki a Kaduna.

A ranar Laraba 23 ga Satumba ne za ayi sadakar uku kamar yadda Musulmai su ke yi. A wannan rana za ayi wa mamacin addu’o’i na musamman.

Shehu Idris ya rasu ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba a asibitin sojoji da ke Kaduna. Gwamna Nasir El-Rufai ya tabbatar da wannan.

Idris shi ne sarkin da ya fi kowa dadewa a tarihin masarautar Zazzau, ya yi shekara 45 a mulki.

KDSG has declared three days of mourning for the late Emir of Zazzau, HH Alh. Shehu Idris. Public offices will open as normal on 21 & 22 September 2020. There will be a public holiday on 23 September to honour his memory. Flags will fly at half-mast during the mourning period pic.twitter.com/8UYEYi4AxC

— Governor Kaduna (@GovKaduna) September 20, 2020

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button