Labarai

Fatal Arrogance ! ‘Yan Ta’adda (Yan shi’ah) Sun Kai ƙara An Ɓata Musu Suna ~ Datti Assalafy

Abin mamaki yanzu nake karanta wani labari cewa wai kungiyar tarzoma na shi’ah wato IMN karkashin jagorancin tsageri Zakzaky sun kai karan wadanda suka shirya film din FATAL ARROGANCE wanda suka nuna shi’ah ta Zakzaky a matsayin kungiyar tarzoma da ta’addanci da take taka dokar kasar Nigeria da yin fito na fito da hukumomin tsaro

Don haka sai suka shigar da kara zuwa gurin babban sufeta Janar na ‘yan sandan Nigeria akan wai ‘yan wasan kwaikwayo na kudancin Nigeria sun bata musu suna, sun alakantasu da ta’addanci

To da farko dai kungiyar IMN ta Zakzaky gwamnatin Nigeria ta soketa, kuma ta haramta kungiyar da duk ayyukanta, sannan gwamnatin Nigeria ta ayyana kungiyar IMN a matsayin kungiyar ta’addanci, wato da kungiyar Shekau Boko Haram da kungiyar Zakzaky IMN duk dayane a cikin dokar Nigeria, babban sufeta janar na ‘yan sanda shi ya sanar da duniya matakin da gwamnatin Nigeria ta dauka akan IMN bayan ta cika dukkan sharadi na zama kungiyar ta’addanci da take barazana ga tsarin mulkin Demokaradiyyah da zaman lafiyar Nigeria

Don haka ya za’ace wai kungiyar ta’addanci tayi kara an bata mata suna???
Shin akwai wani suna mai kyau da ya rage wa kungiyar ta’addanci???
Gwamnati ba zata sauraresu ba, domin kungiyace ta ta’addanci

Akwai wawayen Musulmai daga cikin mu wadanda suke ganin abinda ‘yan wasan kwaikwayo suka yiwa ‘yan shi’ah ba daidai bane, wai Musulunci ake kokarin batawa, wannan maganar rashin hankali ne da cin zarafin Musulunci, shi’ah ba Musulunci zuke wakilta ba, asali ma shi’ah Musulunci suke yaka, idan batanci ne wa Musulunci babu wanda ya kai shi’ah bata Musulunci, tun kafuwarsu a tarihi suke bata Musulunci amma basuci nasara ba, don haka mu bama bawa duk wanda zai bata Musulunci hakuri, kuma duk wanda ya fasa yin batanci wa Musulunci Allah Ya tsine masa albarka kowaye

Don haka bai kamata musulmi ya nuna damuwa ba, abinda ‘yan shi’ah sukayi wa Musulunci shi aka musu, ‘yan shi’ah sunfi kowa shirya fina-finai wajen yin batanci ga mafi alkhairin Musulmai wato Sahabban Annabi da Matansa, Allah ne ya fara daukarwa Musulunci fansa ta sanadiyyar mutanen banza, wannan tsarin Allah ne, wani lokacin idan taimakon Allah ya zo wa Musulunci ko ta hannun kafurai yana iya zuwa da iznin Allah

Anan unguwar gyallesu dake garin Zaria gurin bukin Ashura, kafin Gazwatu Hussainiyya Baqiyyatush-shaidan dakarun Buratai su far musu, ‘yan shi’ah suke tsara wasan kwaikwayo su daure akuya da igiya su mata bakin fenti suna janta a kasa suna dukanta da bulala suna nuna cewa wai Aisha ce matar Annabi Muhammad (SAW) ‘yar Sayyidina Abubakar, matar da suka yiwa sharrin zina Allah Ya wanketa a Qur’ani, karya da sharri sukayi, to amma yau Allah Ya toni asirinsu ta sanadiyyar mutanen banza hankalinsu ya tashi, kadan suka fara gani tsinannu

Yaa Allah Ka mana maganin duk wata kungiyar ta’addanci a Kasarmu Nigeria Amin

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button