Labarai

Dan Polanda Da Wasu 119 Sunyi Tayin Fansar Yaron Da Yayi ɓatanci Ga Annabi

Daraktan cibiyar al’adun nan ta, Auschwitz-Birkenau State Museum in Warsaw, Poland, da ke kasar Polan, Dakta Piotr Cywiński, ya ce shi da wasu mutane 119 sun sadaukar da kansu domin a daure su har na tsawon shekaru goma, matukar dai hakan zai sanya a saki yaron nan wanda ake tsare da shi a Kano a bisa laifin da ya aikata na cin zarafin Ma’aikin Allah.
An kafa gidan al’adun ne a sansanin Oświęcim, a can kasar ta Poland. Cibiya ce ta gudanar da bincike domin tunawa da mutane miliyan 1.1 da suka hada da Yahudawa 960,000, wadanda suka mutu a lokacin yakin Duniya na biyu. kididdiga ta nu na cewa wannan cibiyar ta janyo ra’ayin maziyarta akalla miliyan 2.9 a shekarar 2019.
Kamar yadda LEADERSHIPAYAU ta ruwaito cikin wasikar daukaka karan da suka rubuta wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, Cywiński, dan shekaru 48 da haihuwa, wanda kuma masanin tarihi ne da tattalin arziki, ya ce shi da wasu mutanan su 119 da suke warwatse a sassan Duniyar nan sun amince a yi masu daurin wata guda kowannen su a gidan yarin Nijeriya, domin a saki Omar Farouk, wanda wata kotun shari’a a Kano a watan Agusta ta yanke ma shi hukuncin darin watanni 120 a bisa samunsa da laifin cin zarafin Ma’aikin Allah, a lokacin da suke wani zance shi da wani abokinsa.
Wannan hukunci da kotun ta zartas a kan Farouk ya janyo cece-kuce daga ‘yan Nijerya masu yawa da kuma wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama.
Cikin wasikar mai dauke da kwanan watan 25 ga watan Satumba, 2020, Cywiński ya nemi Buhari da ya yafe wa Farouk a bisa la’akari da karancin shekarun sa.
Masanin tarihin dan kasar ta Poland, ya kuma ma yi alkawarin daukar dawainiyar karatun yaron Farouk matukar dai Buhari ya yafe masa.
Ya zuwa dai ranar Asabar, Shugaban kasan bai bayar da wata amsa ba ga bukatar ta Cywiński a kan Farouk.
Wannan hukunci dai da aka yanke wa matashin ya zo ne kimanin makwanni kadan da wata kotun ta yanke wa wani mawaki mai suna Yahaya Sharif Aminu, hukuncin kisa a can Kano din ta hanyar ratayewa a bisa saminsa da laifin cin zarafin Manzon Allah Annabi Muhammadu (S).
Jihar Kano tana daya daga cikin Jhohin Arewa 12 da suke aiki da shari’ar Musulunci a tare da tafarkin tsarin mulkin kasar.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button