Labarai
Buhari ya yi wa Obaseki na PDP murnar lashe zaɓe
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yaba wa tsarin zaɓen jihar Edo, wanda Godwin Obaseki na PDP ya yi nasara.
Bbchausa na ruwaito a wata sanarwa da mai ba magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya fitar, shugaban ya taya wanda ya samu nasara murna sannan ya buƙace shi da ya nuna halin sanin yakamata da tawali’u a nasarar tasa.
Ya kuma ce alwashin da ya sha kan batun gudanar da zaɓe mai gaskiya da adalci na nan daram.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com