Kannywood
Bidiyo: Yadda Aka Cashe Da Wakar Sunusi II ‘Sarkin Kano’ Ta Naziru Sarkin Waka A Bikin Hanan Buhari
A tsarin da aka ɗauka na bikin da ake yi masa hidimar tarurruka, akan saka sauti domin jin daɗin mahalarta har ma su taka su rausaya.
Cikin waƙoƙin da aka cashe da su a wajen taron bikin Hanan Buhari, akwai wakar mawaƙi Naziru Ahmad mai taken ‘Mata Ku Ɗau Turame’ wadda ya yi wa tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II.
A wani faifan bidiyo na taron bikin wasu da suka halarci bikin, ya nuna yadda matan da suka halarta, da alamu sun ji daɗin sanya waƙar wadda ta kai su ga canza salon rawar da suke takawa.
Ga bidiyon wakar da Sarkin waka nazeer m Ahmad ya wallafa a shafinsa na Instagram.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com