Bidiyo : Gani Ya Kori Ji : Kalli Bidiyon Wannan Ƙaramin Yaro Yana Bayyanin Irin Yaki Da Ta’addancin Boko Haram Da ya halarta
Innalillahi Wa Innaa Ilaihi Raji’unn
Shekaran jiya juma’a Civilian JTF suka samu nasaran kama wannan yaro wanda ya samu horo a kan ayyukan ta’addancin kungiyar Boko Haram bayan ya shigo cikin garin Maiduguri daga jeji
Yaron yayi bayanin irin yakukuwa da ya halarta da Boko Haram, da yadda suke hallaka mutane, da yadda suke samun bayanan sirri daga gurin maciya amanar tsaron Nigeria da suke buya a cikin gari da irin kudaden da ake biyansu, hiran da akayi da yaron ya kai kusan mintuna biyar, amma na yanke bidiyon saboda nauyinsa
Yaron yace babu wani abun da zai faru a Nigeria ba’a sanar dasu a jeji ba, duk wani shiri da hukumomin tsaro suke yi a boye ana tura musu da bayanai da bidiyo daga cikin gari, yace akwai wani soja yana da zama a barikin sojoji dake Maimalari, sojan ne yake tura masu da dukkab bayanan sirri suna biyanshi da kaso 50 na kudin da suke samu
Shafin Datti Assalafy ne ya wallafa,yanzu haka an mika yaron hannun Intelligence officers a Maiduguri, ya kamata a zakulo sojan da yake tura masu da bayanan sirri a koreshi daga aiki, sannan a harbeshi har lahira domin ya zama izni ga masu cin amanar tsaron Nigeria
Wannan abin takaici ne, shiyasa harkan yaki da Boko Haram kowa ba abin yarda bane wallahi, ace wai jami’an tsaro duk shirin da zasuyi domin su farwa ‘yan ta’adda sai an samu wani maciyin amana daga cikinsu ya turawa ‘yan ta’adda da bayanan sirri saboda kudi, wannan babban abin fargabane da tashin hankali
Ya kamata duk sojan da yayi shekara 3 yana yaki da Boko Haram a canzashi, daga manyan har na saman duk a canza su gaba daya, shugaba Muhammadu Buhari ya kori shugabannin su ya maye gurbinsu da sabbin jini, imba haka ba za’a cigaba da yiwa sojoji harin kwanton bauna ana kashe su a banza, kuma yakin ba zai kare ba
Muna rokon Allah Ya tona asirin duk wani maciyin amana da yake taimakon ‘yan Boko Haram ta kowace irin hanya Amin.
Ga bidiyon nan kasa.