Bayanan Sirrin Boko Haram/Iswap A Yankin Baga (Hoto) ~ Datti Assalafy
Idan aka duba wannan hoton, google map ne nayi screenshot daidai gurin da Boko Haram suka yiwa tawagar Gwamnan Borno hari jiya akan hanyarsu na zuwa cikin garin Baga
Harin ya faru ne a daidai Korochara kuma kusa da babban sansanin rundinar sojijin hadin gwiwa na kasashen tafkin Chadi (MN/JTF) wato Daba Magaji, kuna ina ganin nisan dake tsakanin Korochara da Daba Magaji, amma Boko Haram suka iya tare tawagar jami’an tsaron suka kashe 15 a cikinsu
Sannan jama’a ku duba tsakanin sansanin rundinar MNJTF da kauyukan Doro Naira da Kangarwa, wadannan kauyuka sune manyan sansanin kungiyar Boko Haram/ISWAP a yankin Baga amma an gagara isa inda suke, a duk lardin kasar Baga ba su da manyan sansanin ta’addanci sama da Doro Naira da Kangarwa
Duk wani harin ta’addanci da sauran tsare tsaren kungiyar ISWAP daga nan ake shiryawa, duk wani hari da za’ayi a garin Baga, Cross Kauwa, Kukawa, Monguno da saura gurare da duk wani harin kwanton bauna da suke yiwa sojoji ISWAP suna tsarawa ne daga Doro Naira da Kangarwa, kuma maharan daga nan suke fitowa
Ta iya yiwuwa masu iko da tsaron Kasar sun san da wannan ko basu sani ba, to amma wannan shine abinda yake faruwa, kuma shine babban barazanan da yanzu ake fuskanta game da yaki da Boko Haram/ISWAP
Nigeria tana da karfin da zata iya amfani da bama-bamai da sauran makamai masu linzami wanda zata iya kona garuruwan Doro Naira da Kangarwa, ko dabbobi ne suke rayuwa a wadannan kauyuka to ‘yan Boko Haram ne, haka maza da mata manya da yara kanana a kauyukan dukkansu zallan Boko Haram ne a garin, ruguje su da manyan bama-bamai ba laifi bane
Ina yawan zantawa da wasu daga cikin jami’an tsaron sirrin kasarnan akan yadda yaki da Boko Haram yake gudana, ina yawan fadin cewa; jimawa da mukayi muna yaki da Boko Haram ya kamata ace zuwa yanzu mun kai matakin da kafin ace Boko Haram sunyi hari mun sani tunda an san maboyarsu
Na fada cewa ina da mutane na da suka samu horo akan leken asiri, abinda muke bukata gwamnati ta bada kayan aiki, sannan ta dauki nauyi sannan a cika wasu sharuda, amma magana ta gaskiya ba’a ko kulawa
Kasancewar muna zaune cikin Nigeria, na kan zabi nayi shiru akan bayyana wasu sirrukan ‘yan ta’addan wanda zai nuna gazawar wasu masu iko da tsaron kasar saboda wasu dalilai na maslahar kaina, amma ina jin bakin ciki da takaici, saboda Boko Haram ba su fi karfin a kawar da su ba
Da jimawa ya kamata ace zuwa yanzu gwamnatin Nigeria ta shafe babin yaki da ta’addancin Boko Haram sai dai tarihi, amma saboda tsantsar cin amana da rashin kishin kasa na wasu azzalumai da aka basu amana sukaci, ya sa mun kawo zuwa wannan lokaci Boko Haram na cigaba da cutar da mu
Yaa Allah Ka raba tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da maciya amana, Ka nuna mana karshensu da Boko Haram Amin