Sports
Barcelona Ta Rantse Bazata Sayar Da Messi Ba
Advertisment
Mahaifin Lionel Messi da wakilinsa, Jorge, sun gana da shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu, wanda ya shaida musu cewa ba zai sayar da dan wasan Argentina, mai shekara 33 ba. (Marca)
Ganawar farko da aka yi tun bayan Messi ya nemi barin Barcelona ta tashi baram-baram, inda kungiyar ta ce dole ya kammala kwangilarsa ta shekara biyu. (Mundo Deportivo – in Spanish)
Kudin da Barcelona za ta karba idan Messi zai bar kungiyar zai iya zama kasa da euro 100m (£88.8m), in ji jaridar Telegraph.
Sabon kocin Barcelona Ronald Koeman yana so kungiyar ta yi duk abin da za ta iya domin dauko dan wasan Liverpool da Netherlands Georginio Wijnaldum, mai shekara 29. (ESPN)
An gayyaci Manchester United ta sasanta da Bayern Munich kan dan wasan Sufaniya Thiago Alcantara, mai shekara 29. (ESPN)
Aston Villa na fuskantar gogayya daga wurin Newcastle kan dan wasan Bournemouth da Ingila Callum Wilson, mai shekara 28. (Telegraph)
Paris St-Germain ta yi watsi da damar dauko dan wasan Faransa mai shekara 21 Matteo Guendouzi daga Arsenal. (Telegraph)
DC United ta nemi dauko dan wasan Juventus Gonzalo Higuain, mai shekara 32, kuma tana son dauko dan wasan Everton dan kasar Iceland Gylfi Sigurdsson, mai shekara 30. (The Athletic – subscription required)
Kasashen Faransa da Ingila da Sufaniya da kuma China suna son dauko dan wasan Argentina Higuain, a cewar wakilinsa. (Tuttosport – in Italian)
Dan wasan Sufaniya Eric Garcia, mai shekara 19, ya ce zai bar Manchester City idan kwangilarsa ta kare a karshen kakar wasa. (Sun)
‘Yan wasan Arsenal Ainsley Maitland-Niles da Kieran Tierney, dukkansu masu shekara 23, za su ci gaba da zama a kungiyar yanzu bayan kocinta Mikel Arteta ya bayyana karara cewa yana son su zauna. (90mins) tattara bayanai bbchausa
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com