Labarai

Babban Albishir Ga ‘Yan Nigeria Daga Ma’aikatar Sadarwa

Ministan zai gabatar da wannan tsarin ne domin samun dama tare da garabasa ga ‘yan Nigeria wajen koyan sana’o’i iri daban-daban na zamani, da samun ayyukan yi cikin sauki, kuma an tsarashi yadda kowa zai iya koya da kanshi ta hanyar gani a video da rubutu, wannan tsarin yana da matukar mahimmanci ga ‘yan Nigeria.

Wannan tsari yana da saukin fahimta da kuma saukin amfani ga mai aiki da shi, sannan ba sai kana da data a wayar ka ko computer zaka iya shiga tsarin ba, tsarin an raba shi kaso uku:

1. Digital Nigeria
2. NITDA Academy.
3. IBM Digital  For Africa
Kowani tsari yana da mahimmanci, kuma za’a baka certificate bayan kammala training din, ga yadda tsarin yake da yadda za’ayi amfani da manhajan da kuma amfanin su ga ‘yan Nigeria

(1) “DIGITAL NIGERIA”
Shi wannan tsarin yana da fannoni da yawa a tare dashi, zaka koyi sanin menene computer da yadda ake sarrafa ta da kuma sanin manhajoji da computer ke dauke dashi, sannan ta yaya zaka sarrafa su dan ka nemi kudi dasu?
Misali akwai tsari na masu koyo wadanda basu san computer ba kamar haka:

DIGITAL SKILLS……
(a) Yadda zakayi aiki da computer.
(b) Yadda zaka samu bayanai ta yanar gizo.
(c) Yadda zaka bayar da kuma yada bayanai ta yanar gizo.
(d) Yadda zaka kiyaye kanka daga sharrin ‘yan damfara a yanar gizo.
(e) Yadda zaka kir-kiri wani abu da computer.
(f) Yadda zaka kula da manhajar ka a computer.
(g) Yadda za kayi ammani da manhajar Microsoft office.

Sannan akwai tsari na wadanda sun fara koyon computer, da sanin yanar gizo tsarin su yana nan kamar haka;

INTERMIDIATE DIGITAL SKILLS….
(a) Yadda zakayi manhajar computer
(b) Yadda zakayi manhaja HTML da CSS
(c) Yadda hakayi manahaja mai nazari da kanshi
(d) Yadda zakayi ammani java script
(e) Yadda zaka kir-kiri Manhaja

Da kuma tsarin wadanda sukayi nisa da sanin computer da yanar gizo harma da kirkire-kirkiren manhaja da computer, suma ga tsarin su kamar haka;

ADVANCE DIGITAL SKILLS……
(a) Yadda za kayi fani da Data science analytical
(b) Yadda za kayi ammani da HTMAL 5
(c) Yadda za kayi ammani da node.Js
(d) Yadda zaka koyi Netwoking
(e) Yadda zaka koyi kir-kiran manhajar komfuta da na wayar hannu
(f) Yadda zaka koyi aiki duk wani nau’i na kumfuta da manhajar sa.
(g) Yadda zakayi kasuwa da komfuta ta hanyar yanar gizo
(h) Yadda zaka tallata kasuwar ka ta hanyar yanar gizo
(i) Yadda zaka nemi masu sayan kayan ka ta hayar yanar gizo
(j) Yadda zaka bayar da gummmuwa ga gwamnati ta yanar gizo.
(k) Yadda zaka dauki ma’aikatan ka ta yanar kizo.
(l) yadda zaka nemi aiki ta yanar gizo.

(2) “NITDA ACADEMY”
Shi kuma wannan yana da tsari kashi uku wanda masu bangaren zasu amfana dasu, kamar haka;

(a) MDAs Training:- yana da courses da dama.
(b) Students Training:- yanada courses nashi da dama dasuka shafi yan makaranta
(c) General Training:- wannan ta shafi kowa da kowa

(3) “IBM DIGITAL FOR AFRICA”
Wannan tsari ne wanda kamfanin Amurka ke koyarwa domin fahimtar manhajar zamani a Afrika, suma gasu kamar haka;

(a) Yadda zaka koyi yin manhaja da artificia intelligent.
(b) Yadda zaka koyi yin manhaja da data science.
(c) Yadda zaka koyi yin manhaja da internet of things.
(d) Yadda zaka koyi yin manhaja da machine learning.
(e) Yadda zaka koyi yin manhaja da blockchain.
(f) Yadda zaka koyi yin manhaja ta hayar github

Amfanin sa ga ‘yan Najeria:
1. Samun ilimin computer kyauta
2. Samun aikinyi cikin sauki
3. Koyon sana’ o’in Zamani cikin sauki kyata
4. Sanin surrun ‘yan damfara (yahoo boys).
5. Samun arziki cikin sauki da sauri.
6. Samar da kudin shiga wa kada.
7. Bunkasa tattalin arzikin kasa.
8. Rage aiyukan ta’addanci.

Sannan ina so ku fahimci cewar ko wane tsari yana da ‘ya’ya a kasa da shi, sannan kuma in kuka gama kowani tsari za’a baku certificate
Domin shiga tsarin a shiga cikin wannan adireshin na yanar gizo ayi rijista

https://www.digitalnigeria.gov.ng

Idan an shiga cikin website site din zai nuna yadda kowa zai shigar da bayanansa, abi abubuwan a hankali za’a fahimce su, kuma ya kasance kowa yana da Email wanda yake aiki da kuma lambar waya

Kada a manta wannan tsarin yana bukatan wanda yake rike da babbar waya, a kalla wayar da take iya bude manhajar WhatsApp, kuma tana iya bude application na Opera da Google Chrome, sai kuma wanda yake da computer, zai fi samun saukin koyon abubuwan, ‘yan Arewa kada kuyi wasa, kowa ya shiga ya cika don a amfana, wanda bai gane ba ya tambayi na kusa dashi masani akan fasahar yanar gizo don karin bayani

Wannan aiki ne da zai gudana kyauta karkashin jagorancin Maigirma Babban Ministan Sadarwa Dr Isah Ali Ibrahim Pantami da taimakon hukumar bunkasa fasahar sadarwan zamani na Nigeria NITDA Nigeria karkashin jagorancin Babban Darakta Janar Malam Kashif Inuwa Abdullahi bisa umarnin Maigirma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan kudurin da yake da nashi na rage yawan ‘yan Nigeria masu fama da talauci tare da habbaka tattalin arzikin Nigeria

Muna rokon Babban Sarki Allah Ya taimakesu, Ya saka musu da mafi alherin sakamako, Ya sa ‘yan Nigeria su amfana da wannan shirin
Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum,datti Assalafy ne yayi kokarin tattara wannan labari

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button