Labarai
Baban mai kuɗin duniya ya rasu
Advertisment
Mahaifin Bill Gates, ɗaya daga cikin attajiran duniya wanda ya samar da kamfanin Microsoft ya mutu.
William Henry Gates II ya mutu a ranar Litinin ya na da shekara 94.
Cutar Alzheimer da ke shafar ƙwaƙalwa ce ta yi sanadi mutuwarsa, kamar yadda iyalansa suka tabbatar a wani labarin da jaridar New York ta wallafa.
Gates Babba tsohon soja ne kuma ya kafa kamfani da ke harkokin shari’a, kamar yadda tarihinsa ya nuna.
Advertisment
Bbchausa ta ruwaito bill Gates mai shekara 64, ya ce sun yi babban rashi kuma zai dauke su tsowon lokaci su na jimamin mutuwar mutumin da ya yi tasiri a rayuwar mutane da dama.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com