Labarai

Ƙarin Kuɗin Man Fetur Ya Zauna Daram, Ba Za A Rage Ba, Inji Buhari

Daga Comr Bashir Suleiman Bash Dambam

Shugaba Buhari ya ce ba a za rage ƙarin kuɗin litar man fetur ba, domin idan gwamnati ta ci gaba da biyan tallafin rarar mai, to tattalin arzikin Najeriya zai shiga garari nan gaba.

Mataimakin Shugaban Ƙasa ne ya sanar da wannan bayani, a madadin Shugaba Buhari, yayin da ya wakilce shi a taron kwanaki biyu na Bitar Ayyukan Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya Na Shekara-shekara, a Ɗakin Taro na Fadar Shugaban Kasa.

Buhari ya ce annobar cutar Korona ta dankwafar da ƙarsashin da tattalin arzikin ƙasar nan ke da shi, ta yadda kudade sun yi ƙaranci a aljihu da asusun gwamnatin tarayya.

Ya ce babu wadatattun kuɗaɗen da za a rika ayyukan kasafin kuma kuzarin da gwamnati ke da shi ya ragu, saboda ƙarancin kuɗaɗen.

Buhari ya ce daya daga cikin matakan da gwamnatin sa ta dauka bayan barkewar cutar Coronavirus a cikin Maris, shi ne batun cire kudin tallafin mai, saboda a kasuwar duniya da ake takama din ma, farashin danyen mai ya karyar sosai.

Sai dai ya ce gwamnatin sa na nan ta na aiki tukuru domin saukake wa ƴan Najeriya kuncin fa za su shiga da takura sakamakon cire tallafin, wanda shi ne ya haifar da ƙarin farashin man fetur ɗin.

Za a fuskanci gagarimar matsalar rashin kudi idan gwamnati ta ce ta koma kan tsohuwar al’adar ƙayyade farashin fetur ko biyan kudin tallafin mai da kan ta.

Na farko ma dai tukunna, idan aka yi hakan, to an koma biyan tallafin mai kenan kamar yadda aka riƙa wannan gagarimar kasassabar a baya. A yau kudaden shiga sun ragu da kashi 60 bisa 100. Gaskiya ba za mu iya ci gaba da tafiya a haka ba.

“Idan Aka Rage Kuɗin Fetur, Layin Mai Zai Dawo” – Buhari

Matsala ta biyu kuma gagarima, ita ce, idan aka rage kuɗin mai, to za a koma ‘yar-gidan-jiya, wato tsayawa dogon layin shan maj, wanda a wannan gwamnatin yanzu ya zama tarihi.”

“Yan Kasuwa Suka Yanka Farashin Litar Mai, Ba Gwamnati Ba”

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin da Karamin Ministan Fetur, Timipre Sylva, ya bayyana cewa ‘yan kasuwa suka yanka farashin litar mai, ba Gwamnatin Buhari ba.

Kuma ya bayyana dalilin da ya ce Buhari ba zai sa baki a rage kuɗin ba.

Karamin Minsiatan Harkokin Man Fetur, Timipre Sylva, ya jaddada cewa ba Gwamnatin Tarayya ce ke yanka farashin da ake sayar da litar man fetur a ƙasar nan ba.

Sylva ya bayyana wa manema labarai haka dangane da haushi da damuwar da dimbin ‘yan Najeriya ke ci gaba da nunawa a kan karin kuɗin litar man fetur da aka yi.

Farkon makon nan ne Hukumar Kayyade Farashin Man Fetur ta maida litar fetur farashin sari ga ‘yan kasuwa kan Naira 151. Su kuma dillalan suka kara naira 10 ladar jigilar kowace lita, inda suke sayar da lita daya naira 161.

Sylva ya ce abin takaici ne ganin yadda jamai ke dora wa Gwamnatin Buhari laifi.

Ya ce har yanzu muradin wannan gwamnati shi ne ta samar da saukin rayuwa ga al’ummar Najeriya.

“Kun dai san Shugaba Muhammadu Buhari shi ne gadon bayan goyon marayu, musamman talakawan Najeriya.” Inji Sylva.

“Babu yadda za a yi haka kawai Buhari ya goyi bayan a kara farahin fetur, har sai fa idan tura ta kai bango, ya ga babu wata mafita idan ba a yi karin ba.

“Kun kuma ga yadda cutar Coronavirus ta karyar da farashin fetur ya koma kamar farashin ruwan aski.” Inji Sylva.

Ya ce karin ya zama dole, saboda gwamnati ba ta iya biyan kudaden tallafin man fetur.

Sai dai kuma yayin da kowa ke kokawa wannan karin kudin fetur da na wutar lantarki, jam’iyyar APC cewa ta yi Gwamnatin Buhari ta kara kudin fetur da wutar lantarki don ‘yan Najeriya su ji dadi.

Jam’iyyar APC ta ce Gwamnatin Tarayya ta kara farashin wutar lantarki da na man fetur domin jin dadin ‘yan Najeriya.

Wannan bayani ya fito ne a matsayin raddi ga jam’iyyar PDP, wadda a ranar Laraba ta shiga sahun ‘yan Najeriya masu sukar karin farashin fetur da na hasken lantarki.

Cikin sanarwar da PDP ta fitar a ranar Labara bayan gwamnati ta fito da sabon farashin sarin litar fetur naira 151 daga NNPC, jam’iyyar PDP ta ce ba ta yarda da karin ba.

“Kun ce a kori PDP saboda a gwamnatin ta ana saida fetur naira 87. To ga shi nan a karkashin APC, tun ba a je ko’ina ba lita daya ta koma naira 161.” Inji PDP, cikin sanarwar da Kakakin Yada Labarai Kola Olagbondiyan ya fitar.

Gwamnatin Buhari ta kara kudin fetur kwanaki biyu bayan nunka kudin wutar lantarki daga naira 30.36 mitar wuta daya, zuwa naira 66 mita daya.

A na ta martanin jam’iyyar APC ta ce an yi wannan kari ne saboda lalubo hanyoyin da ‘yan Nammjeriya za su samu saukin rayuwa.

A sanarwar da Mataimakin Sakataren Yada Labarai, Yekini Nabena ya fitar, APC ta ce duk wannan galauniya da ake fama da ita, ta samo asali ne daga matsalar da mulkin PDP na shekara 16 ya jefa Najeriya.

“Rashin kunya ce da PDP ta fito ta na sukar karin farashin fetur. Domin ita ce silar shigar Najeriya cikin wannan matsalar. Me zai hana su dawo da kudaden tallafin man fetur din da suka danne a tsawon shekaru 16 su na mulki.”

Tuni dai wannan kari ya haifar da maganganu, har mutane da dama na tuna mulkin Jonathan.

Karin farashin fetur da na wutar lantarki, ya zo a daidai lokacin da tsadar kayan abinci na neman abincin ya gagari talaka a Nijeriya.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button