An kama wasu mata hudu da ake zargi da sayar da jariri kan kudi N1.5m (Hoto)
Jami’an hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP) sun cafke wasu mata hudu bisa zargin sayar da sabuwar haihuwa kan kudi N1,500,000.
An gabatar da matan a gaban manema labarai a ranar Alhamis, 3 ga Satumba. A cewar jami’an NAPTIP, biyu daga cikin matan, Bernadette Ihezuo da Cecilia Onyema, ma’aikatan gwamnati ne a Ma’aikatar Kudi ta Tarayya Abuja, da Ma’aikatar Noma da Raya Karkara, bi da bi. Wanda ake zargi na uku, Okasi Ekeoma, an ce kanwar Onyema ce, yayin da ta hudu da ake zargin ta itace kakar jaririn Harrieth Nmezi da ke zaune a jihar Imo.
Sources: Linda Ikeja |
A cewar jami’an NAPTIP, yarinyar ta yi ciki yayin da take tare da mahaifiyarta sannan ta kai ta gidan Onyema inda take zaune har sai da ta haihu. Kai tsaye bayan haihuwar, sauran matan suka karbe yaron daga hannun yarinyar sannan suka sayar da jaririn.
An kama su ne bayan wata sanarwa da wasu jama’a suka karba.
An kubutar da jaririn yayin da wadanda ake zargin suka amsa aikata laifin, kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su a kotu.