Uncategorized

ABIN AL’AJABI: Motar jigila ta nutse cikin gulbi da fasinjoji a Jihar Sakkwato

Kafar Sokoto Tracker ta samu rahoton cewa wata motar jigila da ke dauke da fasinjoji da ba’a tabbatar da adadin su ba, ta nutse cikin gulbin Zanzanu dake Karamar Hukumar Kware.

Lamarin ya faru ne a daren jiya Alhamis, yayin da motar da ke dauke fasinjoji ta fado daga kan gada.

Wani da lamarin ya faru a gaban shi ya bayyana cewa “tun lokacin da lamarin ya faru har kawo yanzu, hukumomi sun kasa gano inda motar take ballantana a ceto mutanen”.

Ya kara da cewa “dukkan alamu sun nuna cewa lamarin ya fi karfin hukuma”.

Har zuwa yanzu, Juma’a, Hukumar NEMA na ta kokari wajen gano mutanen da wannan iftila’in ya afka wa.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA