Kannywood

A ra’ayina A’isha Buhari tafi Shugaba Buhari dacewa da zama shugaban kasa ~ Inji Umma Shehu

Advertisment

Tauraruwar fina-finan Hausa, Umma Shehu ta bayyana cewa a ra’ayinta, Uwargidan shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari ce tafi shugaban kasar, Muhammadu Buhari dacewa da zama shugaban kasa.

Umma ta bayyana hakane ta shafinta na sada zumuntar Instagram inda ta yi tambaya ga masoyanta cewa shin wa yafi dacewa da zama shugaban kasa taakanin Shugaba Buhari da matarsa A’isha Buhari?

Umma tace a Ra’ayinta A’isha Buhari ce tafi dacewa saboda “Tana Son Jama’a kuma tana taimakon Al’umma tunda baba Buhari ya hau Mulki wa kuka taba ji ya taimakawa kila nice ban sani ba”, a cewar Umma.

Hutudole ne na ruwaito,ta kuma kara da cewa, Amma zuciyarta na tausayin talakawa dan tayi tayi a gyara amma yace dakin girkine mazauninta da gidansa, tace amma tasan uwargidan shugaban kasar na da zuciya me kyau.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button