Labarai

Zuwa da karamin yaro masallachi Hakimin Rimi dake Jihar Katsina yasa An Lakadawa dattijo mai Shekaru Tamanin 80 dukan tsiya

Advertisment

 Yadda wani hakimi a jahar Katsina ya sa aka lakadawa wani tshohon soja Mai kimanin shekaru 80 duka, aka Kuma tsare shi tsawon kwana 3, a dalilin Yana zuwa da karamin yaro masallaci.

wannan abun takaici ya faru ne, a garin Rimi dake jahar Katsina, bayan da wasu mutane Suka nemi cewa, wannan tsohon soja Mai suna (Yusuf Soja) ya daina zuwa da karamin yaro a masallaci, saboda Yana Yi musu rashin ji, shi Kuma ya ce ba zai daina zuwa da shi ba, saboda ko a lokacin manzon Allah (saw) Ana zuwa da yara masallaci. A dalilin haka, sai suka Kai kararsa ga hakimin Rimi, Wanda a nan ma ya tabbatar wa da hakimin cewa ba zai daina zuwa da yaro masallaci ba,

Jaridar Shafin mikiya a Facebook ne ta ruwaito haka,tunda shari’ar musulunci ba ta hana ba, hasali ma, umarni ta yi da a koya wa Yara kanana sallah. Don haka sai hakimin ya ce ya raina shi, ya sa dogarawa Suka yi ta dukan sa da bulali, sannan aka tsare shi a fadar hakimin tun safiyar asabar 08/08/2020, har zuwa maraicen ranar litinin 10/08/2020 aka sake shi ya koma ga iyalansa.

   Kafin cin zarafin wannan tsohon soja, matarsa aka fara cin zarafinta, Mai suna (Karima Yusuf) Mai kimanin shekaru sittin da haihuwa, inda hakimin ya sa aka lakada ma ta duka, a sakamakon ta ki amincewa, wani makwabcin filinta ya yi gini akan santa/titi. A dalilin wannan cin zarafi ne, ta Kai koke, a Hukumar Kare hakkin dan’Adam ta kasa reshen jahar Katsina. watau (National Human Righcommission) Wanda tsawon wata bakwai ko takwas da Kai wannan koke, amma har yanzu babu wani takamaiman mataki da Hukumar ta dauka, na bi ma ta hakkinta, to Kuma wannan ba bakon abu ba ne a Najeriya idan ka ga hukumomi na azarbabi a kan lamari, za ka samu talakka ne Wanda ba ya da galihu ya aikata wani abu.
  Wannan dattijo Wanda ya sadaukar da rayuwarsa, ya Yi yaki don samun zaman lafiyar Najeriya, Wanda har yanzu akwai karfe a jikinsa, a dalilin harbin bindiga a lokacin yakin Biyafara, bai cancanci a wulakanta shi Kamar haka ba, Kai duk Wanda ya Kai shekaru wannan dattijon ko bai ba kasa wata gudummuwa ba, ya wuce a buge shi.

Advertisment

    Wannan cin zarafi, da aka Yi wa wannan tsohon soja, to cin mutunci ne ga dukkan tsofaffin sojojin Najeriya, Kai har ma da masu ci yanzu.
  Ina kungiyar tsofaffin sojojin take?
  Ina kungiyoyi masu rajin Kare hakkin bil’adama suke?
  Ina Yan jaridu suke?
  Ina lauyoyi masu taimakawa mararsa karfi?
  ku zo ku taimaki wannan bawan Allah, don tabbatar da adalci akan lamarinsa. Saboda taimakon Wanda aka zalunta wajibi ne, sannan Kuma a hana azzalumi yin zalunci, shi ma wajibi ne.

   Daga karshe Muna rokon Allah madaukakin sarki ya kawo wa al’ummar Rimi karshen wannan zalunci da masarautar Rimi
ke yi musu da gaugawa, saboda duk fadin jahar Katsina babu masarautar da ke zaluntar al’umma Kamar ta Rimi.
Ga mai son Karin bayani ga lambar wayar babban Dan dattijon.
 Aminu Yusuf
07068055705

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button