Sports
Zanga-zanga Ta Barke A Birnin Paris Bayan Kungiyar Kwallon Kafa Ta P.S.G Ta Sha Kashi A Hannun Munich (Hotuna)
Advertisment
Fusatattatun magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta P.S.G a birnin Paris na kasar Faransa sun fito zanga-zanga don nuna rashin jin dadin su da rashin adalcin da Alkalin wasa ya yi wa kungiyar.
A jiya ne ankayi wasa tsakanin Bayern Munich da P.S.G wanda ta tashi ci daya mai ban haushi 1-0 kenan wanda coman ya zura kwallon a ragar psg misalin minti 59 bayan an dawo hutun rabin lokaci.
Daga bisani zanga-zangar ta rikide ta koma tarzoma inda suka ringa kone-kone da fashe-fashe kafin ‘yan sanda su tarwatsa su.
Psg ta Kai Shekara hamsin bata kawo wannan matakin ba ga masu sharhi da kididiga akan harka wasa ni.
Rundunar ‘yan sanda a birnin Paris ta sanar da ta kama mutane 100 a cikin masu zanga-zangar. Kuma za ta zartar da hukunci da ya dace da su.
Advertisment
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com