Yanzu-Yanzu:Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya saki sakon Murya inda yayi Allah wadai da hukuncin kisan da aka yankewa wanda yawa Annabi(SAW) Kalaman Batanci
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kungiyar Boko, Abubakar Shekau a karin farko shima ya tsoma baki cikin shari’ar da aka yankewa matashinnan na Kano, Umar Sharifai da aka samu da laifin kalaman batanci ga Annabi.
Kotun Shari’ar Musulunci dake Hausawa, Kano ta ya kewa matashin me shekaru 22 hukuncin kisa ta hanyar rataya, lamarin da ya jawo cece-kuce, musaman daga Kudancin kasarnan, hutudole ya kawo muku yanda a baya shekau ya saki Bidiyo yanawa gwamna Zulum barazana.
A wannan karin, HumAngle ta ruwaito cewa shekau ya saki sakon Murya inda yayi Allah wadai da hukunin kisan da aka yankewa matashin inda yace bai da banbanci da wanda suka yanke masa hukuncin. Hutudole ya fahimci cewa Shekau dai cikin abinda bai fi sati 1 ba yayi magana sau 2 kenan wadda ya saketa ga jamaa.
JUST IN: Abubakar Shekau, in a new audio, has condemned the Kano State death sentence. According to the embattled #BokoHaram leader, there is no difference between the ‘blasphemer’ and those who sentenced him to death. More details coming soon. pic.twitter.com/mpENRoSEaj— HumAngle_ (@HumAngle_) August 12, 2020
Advertisment
HumAngle dai ta bayyana cewa nan gaba kadan zata saki cikakken bayani game da wannan sakon muryar na Shekau.