Labarai

Yanzu – Yanzu : Sojojin Kasar Mali Sunyi Juyin Mulki A Kasar Mali

Sojojin Kasar Mali sunyi juyin mulki a kasar Mali, sun kama shugaban Kasar shugaba Ibrahim Bubakar Kaita, sun kuma kame babban birnin kasar Bamako da fadar mulkin kasar bayan rikicin siyasar kasar yaki karewa.

Manyan kwamandojin yakin Kasar Mali da General-General din sojin Kasar  irin su Manjo Janar Fanta Mady Dembélé, Kanar Sadio Camara da kuma Col Malick Diaw ne suka kifar da gwamnatin shugaba Bubakar Kaita, wanda yanzu haka ba’a san inda suka yi dashi ba.

Datti Assalafy yayi ruwaito ,KungiyarECOWAS tayi ta kokarin sasanta rikicin siyasar Kasar, ta tura tsohon shugaban Nigeria Goodluck Jonathan yana zuwa Kasar har sau biyu, sannan uwa uba ta tura shugaban Kasar mu Nigeria Muhammadu Buhari da sauran shugabannin kungiyar ECOWAS amma duk a banza

Wannan babban barazana ne wa tsarin mulkin Demokaradiyyah, kuma wannan zai kara bude kofar rikici mai tsanani a Kasar, dama akwai wani boyayyen ajanda da ake so a cimma, akwai kofar barna da ake so a bude

Allah Ya sauwake

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button