Labarai

Yanzu – Yanzu : An Sanya Dokar Ta Bata ci A Gambia

Advertisment
Shugaban Gambia Adama Barrow ya sanya dokar ta baci a fadin kasar na tsawon kwana 21 sakamakon karuwar annobar cutar korona a kasar.
Shugaban ya ce iyakokin kan tudu da sararin samaniyar kasar za su ci gaba da kasancewa a rufe, sai dai za a bar jirgin daukar kaya ya ci gaba da aiki, da jami’an diflomasiyya da kuma masu zuwa kasashen waje neman magani.rahoton bbchausa
Kasar tana da masu dauke da cutar kusan 700 kuma tuni 16 cikinsu suka mutu.
Mataimakin shugaban kasar da kuma wasu ministoci uku na cikin masu dauke da cutar, sai dai da aka yi wa shugaban kasar gwaji a ranar Litinin sakamakon ya nuna baya dauke da cutar.
An rufe duka wuraren ibada a fadin kasar, amma ana barain ‘yan shekarar karshe a makarantun fadin kasar suje domin rubuta jarrabawa wadda za a fara daga 17 ga watan Agusta.
Ana kulle duka shaguna da kasuwanni domin a rika yi musu feshin magani ko wacce ranar Lahadi
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button