Uncategorized

Tasirin Bambamcin Shekaru A Zamantakewar Aure

Duk da yake ba haramun bane a addinance da kuma al’adance namiji ya auri wacce zai yi jika da ita. Ko kuma mace ta auri dan cikinta. Hakan ma yasa ba a cika hango irin tasirin da bambamcin shekaru zasu iya bada gudummawa a zamantakewarsu na aure ba.

Mutane sun tafi akan muddin akwai soyayya a tsakanin masoya to bambamcin shekaru ba matsala bane. Sai da a ɗabi’ance abun ba haka yake ba a zamantakewa irin na aure.

Masana halin ɗan Adam sun yi sabani game da tazaran shekaru da za a iya samu tsakanin ma’aurata. Wasu na gani kada bambamcin shekaru su wuce daga biyar zuwa goma. Wasu na ganin daga goma ne zuwa sha biyar. Sai masu ganin a’a daga sha biyar ne zuwa ashirin. Koma ma dai wannene kuka zaba, tabbas bambamcin shekaru yana da tasiri ga masoyan da suke bukatar cimma burin rayuwar aure na mutu ka raba.

Bari mu fara da macen data girmi wanda zata aura. Anan muddin shekarun nasu yana da tazara sosai suna iya fuskantar Matsalolin da nan gaba zai iya hana musu zaman aure mai daɗi da amana.

☞ Matsala ta farko itace gadara: Mace koda bata da kudi muddin ta girmi mutum to fa tana so lalle ta nuna wannan girman nata. Ita mace koda tazaran shekaru biyu zuwa biyar namiji ya bata, ita bata ganin wannan a wasu shekaru ne da zai baiwa namiji damar nuna mata fifiko. Bare kuma ace ta hada biyu da shekaru da dukiya. Don haka yana da wuya shi wannan mijin nata ya samu biyayya a gareta 100/100 kamar yadda ake son ganin macen aure tabi mijinta.

☞ Matsala na biyu shine zai yi wuya ta iya yiwa mijin ta hidimar da ya kamata na tsakanin miji da mata irin abunda ya shafi girke girke, gyaran dakin miji ba tare da ta saka wani ko wata mai taimako sun mata ba.

Duk da yake a halitta ita mace tana kara girma ne take kara son jima’i. Amma akwai shekarun da idan ta kai bazata iya gamsar da mijin ta ba amma kuma a ranta tana sha’awar abun. Don haka idan aka zo wannan lokacin shi kuma Namiji zai iya bukatarta yadda bazata iya biya masa ba saboda shekaru.

Duk namijin da ya soma auren macen data bashi tazaran shekaru masu yawa, yana da matukar wahala ya iya kara wani aure koda kuwa yana son hakan. Ita mai yawan shekaru ko itace ta shigo ta tarar da wata burin ta shi ne ta kwace mijin sai yadda tayi dashi ko kuma tayi silar korar wacce ta tarar. Idan hakan ya faru namiji zai tsinci kansa a zinace zinace ne maimakon ya samu damar kara wata matar da zata rika biya masa bukatar sa.
Babban matsalar namiji ya auri mace wacce ta girmeshi da shekaru masu yawa shine rashin tabbas na haihuwa.

Akwai matan da haihuwar su na tsayawa ne da wuri yadda duk zaman da zaku yi yana da wuya ta haihu. Hakan kuma zai iya shafar rayuwar namiji a matsayin wanda yake bukatar haihuwa.

Sai dai kuma waɗannan Matsalolin ba ana nufin shi namiji mai ra’ayin auren mace data masa fintinkau a shekaru bazai aureta bane. Kawai ana hankaran dashi ne akan su domin yin la’akari dasu yasan da su kamin ya yanke hukuncin auren mai wannan shekarun a matsayin matarsa.

Sai dai kuma duk da wadannan Matsalolin da muka ambata. Auren macen data girmemaka a shekaru yana da alfanu. Ta bangaren yiwa miji hidima ba tare da ta saurare shi ba muddin tana dashi. Akasarin mata masu shekaru suna da wannan sai dai dole namiji kuma ya zama yana da haƙurin da zai iya jimirin gõri.

A darasi na gaba nan ma zamu haskowa mata Matsalolin auren na miji mai yawan shekaru.

#tsangayarnalam

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button