Labarai

Subhanilillahi ! Rundinar Sojojin Nigeria Ta Kalubalanci Gwamna Zulum ~ Datti Assalafy

Rundinar sojin Nigeria ta zargi Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Zulum da laifin sanyaya gwiwar dakarunta dake yakar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar, ta hanyar tuhumarta da zarge-zarge marassa tushe.

A watan da ya gabata, Gwamna Zulum ya caccaki sojojin, tare da tuhumarsu da kaiwa tawagarsa farmaki a lokacin da ya kai ziyara a garin Baga, sannan Gwamnan yayi barazanar hada dakarun ‘yan sanda da mafarauta don baiwa garin na Baga tsaro, idan har sojoji suka gaza.

Sannan Gwamna Zulum yayi zargin cewa dalilin da yasa sojoji suka hana mutane komawa gidajensu saboda manyan sojojin suna noma a gonakin su, zargin da akace shugaban sojojin Nigeria Janar Buratai ya sa ayi bincike

Sai dai bayan kammala bincike, Manjo Janar Felix Omoigui, mataimakin babban kwamandan Operation Lafiya Dole, yace babu gaskiya a duk zargin da gwamna Zulum ke musu, kuma kalaman gwamnan na sanyaya gwiwar dakarunsu dake kokarin fatattakar kungiyar Boko Haram

Tsakani da Allah jama’a ta yaya Gwamna Zulum zai sanyaya gwiwar dakarun sojin Nigeria da suke bakin daga, idan ya sanyaya gwiwarsu a yakin da sukeyi ribar me zai samu? mutumin da yake son a kawar masa da Boko Haram daga garinsa, yace ya sadaukar da rayuwarsa, ko dai Boko Haram su ga bayanshi ko kuma shi ya ga bayansu, yau kuma shi za’a zarga da laifin sanyaya gwiwar sojoji?

Haba jama’a!, ina miliyoyin Naira da Maigirma  gwamna Zulum yake bayarwa domin ya karfafa gwiwar dakaru? hatta ranar da ya shiga garin Baga aka masa hari ai ya bada miliyoyin Naira don ya karfafa gwiwa, mun san sirrin fa, amma yau shi ake zargi da sanyaya gwiwa kawai don ya fadi gaskiya, sanyaya gwiwar jami’an tsaro a fagen daga babban laifi ne fa, ku san daya yake da cin amanar tsaron Kasa

Wannan babban kalubale ne wa shugaba Buhari, abinda ya kamata shugaba Buhari yayi shine ya kafa wani kwamitin sirri mai zaman kansa, su gudanar da cikakken bincike, duk wanda aka samu da laifi to a hukuntashi, kuma a sanar da duniya, ta hakane za’a gane waye babban makaryaci maciyin amana tsakanin Gwamna Zulum da wadannan mutane

Amma da wahala shugaba Buhari yayi haka, domin da alama abin yafi karfinsa, ita dai gaskiya dayace, duk karfin mutum da karfin ikonsa wajen kokarin boye gaskiya wallahi karshen al’amari sai gaskiya tayi halinta watan watarana

Yaa Allah Ka kare Maigirma gwamnan jihar Borno daga dukkan sharri da makircin makirai Amin

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button