Sako Zuga Ga Ali Nuhu Kan Bude Cinema ~ Datti Assalafy
Kamar yadda BBC Hausa suka hada rahoton, jarumi Ali Nuhu yana tunatar da gwamnatin Nigeria game da gina musu sinima, har yake cewa bai ga dalilin da zaisa ba za’a gina ba
Jama’a idan kun tuna a wa’adin farko na mulkin shugaba Buhari akayi yunkurin gina katafaren gidan sinima a birnin Kano da kudin gwamnatin tarayya domin a fadada harkan wasan kwaikwayo da sauran mu’amala mai kama da haka
A lokacin an tafka muhawara sosai, mun fito tare da Malamai muka kalubalanci yunkurin, saboda illolin da yake tattare dashi yafi alherinsa, a dayan bangare baragurbin musulmai ‘yan boko aqeedah da karuwai da duk wasu nau’i na mutanen banza suka goyi bayan gina sinimar, daga karshe Allah Ya kunyatasu
Shekara uku kenan zuwa hudu yanzu da faruwar wannan abin, sai gashi Ali Nuhu ya sake taso da batun, a cikin ‘yan Hausa film Ali Nuhu yana daga cikin wadanda suke burgeni a shekarun baya da nake kallon hausa film, ina kyautata masa zato, domin ba jahili bane
Malam Ali Nuhu shekarunka sun fara nisa, naji hiran da akayi dakai kwanakin baya can a BBC Hausa kana cewa nan da wasu shekaru kadan kana fatan ka samu jika, wato ‘yarka ta kai aure zaka aurar da ita, duk abinda kake nema a duniya na rufin asiri Allah Ya baka, abinda ya rage maka a yanzu shine neman kusanci da Allah Madaukakin Sarki
Ali Nuhu idan ka goyi bayan gina Sinima baka san girman barnan da zata haifar ba, don ba shakka za’a mayar da sinimar gurin cin kasuwa da dandali na manyan kungiyoyin ‘yan Luwadi, Madigo da Mazinata, a hakan ma babu sinimar yaya aka kare ballantana an gina cibiyar da zata hada kowani irin ‘dan iska da ‘yar iska marassa kunya? ya kamata kayi tunani, ka tuna da mutuwa Malam Ali
Allah Ya rufa asiri