Labarai

Nayi Babban Shiri Na Kawo Karshen Cin Hanci Da Rashawa A Nigeria ,Mutane Zasuyi Mamaki. ~ Buhari

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da kawo tsare tsare da zasu kawo karshen cin hanci da rashawa a kasar

– Shugaban kasar ya bukaci hafsoshin tsaro da shuwagabannin hukumomin tsaro da su samar da kyakkyawan tsari da zai kawo karshen matsalolin tsaro a kasar

– Ya ce akwai bukatar ayi aiki kafada-da-kafada domin kasar ta tsaya da kafafunta don cimma kudurorin da aka shimfida su

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada cewa gwamnatinsa na kan turbarta na yaki da cin hanci da rashawa, da yiwa dukiyar al’umma zagon kasa.

Shugaban kasar ya yi wannan bayani ne a taron bukin yaye daliban aji 28 na kwalejin tsaro ta kasa a ranar Alhamis a Abuja.

Da ya samu wakilcin ministan tsaro, Bashir Magashi, ya ce har yanzu akwai sauran aiki wajen farfado da tattalin arzikin kasa, kamar daukar aiki, kawar da talauci da sauransu.

“Dangane da cin hanci da rashawa kuwa, a yanzu, akwai shirin da muka yi na zai taimaka mana waje yaki da rashawa ba tare da jin tsoron duk wanda zata rutsa da shi ba,” cewar Mr Buhari.

Legithausa na ruwaito,Shugaban kasar ya bukaci hafsoshin tsaro da shuwagabannin hukumomin tsaro da su samar da kyakkyawan tsari da zai kawo karshen matsalolin tsaro a kasar.

Mr Buhari ya ce duk da cewa kasar na fuskantar matsaloli da suka hada da rashin tsaro, rashin aikin yi, annobar COVID-19 da sauransu, kasar na taka muhimmiyar rawa a dukkanin fannonin.

“Duk da wadannan matsalolin, har yanzu yakininmu akan kasar bai canja ba. Muna da kyakkyawan shiri da zai kai kasar tudun mun tsira,” a cewar sa.

Ya ce akwai bukatar ayi aiki kafada-da-kafada domin kasar ta tsaya da kafafunta don cimma kudurorin da aka shimfida su.

A wani labarin; wata mata mai shekaru 53, Hajara Ismail, ta bayyana takaici da bacin ranta akan yadda ‘yan sandan ‘Township’ a jihar Bauchi suka kashe mata yaronta bayan azabtar da shi.

Ta bayyana cewa sun kama yaron ne tare da wasu abokansa da zargin suna satar kajin wani jami’in ‘yan sanda da yayi ritaya a garin.

A zantawarta da jaridar Punch, Hajara Ismail, mahaifiyar Ibrahim Kampanlala, ta labarta cewa a ranar Juma’a ne ‘yan sandan suka kawo gawar Ibrahim gidan, ana tsakiyar bikin kanwarsa.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button