Labarai

MATSALAR FYADE: Uwargidan Gwamna Elrufai Ta Yi Dirar Mikiya A Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Domin Neman Samar Da Dokar Hukuncin Kisa Ko Dandaka Ga Masu Aikata Fyade

Advertisment

Uwargidan Gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Ummi Elrufai a yau Litinin ta yi dirar mikiya a majalisar dokokin jihar Kaduna domin neman samar da dokar hukuncin kisa ko dandaka ga masu aikata fyade.

Uwargidan Gwamnan wadda ta ce akalla ana samun laifin fyade ga kananan yara kusan sau biyar a rana a Kaduna, ta ce zartar da irin wannan hukuncin zai zama darasi ga ‘yan baya.

“Na zo nan ne domin ganin yadda ‘yan majalisun za su yi gaggawar yin gyara kan dokar fyade. Saboda kullum hakan na faruwa akan yara kanana da manya. Matanmu da yaranmu suna bukatar kariya don haka na zo nan domin ganin an yi gaggawar amincewa da dokar.

“Tuni dama Gwamna yana iya kokarinsa don ganin ya baiwa kowane jinsi na mazaunan Kaduna hakkinsa.

“A kullum muna samun matsalar fyade kusan biyar a fadin Kaduna. Ina fadin hakan ne saboda ina aiki kafada da kafada da kungiyoyin da suke yaki da fyade a Kaduna.

“Don haka ina ganin idan aka samar da wannan doka matanmu da yaran mu na Kaduna za su samu kariya sabanin abubuwan da muke gani a yanzu. Don haka ne muke kira ga ‘yan majalisun mu da su samar da tsattsaurar doka kamar hukuncin dandaka ko kisa ga wadanda suka aikata fyade ko suka yi yunkurin yi, cewar uwargidan Gwamnan.

A yayin da yake mayar da martani, Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Honarabul Yusuf Zailani ya nuna damuwarsa kan yadda matsalar fayde ke kara kamari, inda ya sha alwashin za su yi gaggawar sanyawa dokar hannnu zuwa nan da mako mai zuwa.

Rariya na ruwaito,Honarabul Zailani ya kara da cewa wannan shine karo na farko da matar Gwamna mai ci ta tsoma kanta cikin irin wannan doka mai muhimmanci, wanda har ya sanya ta yin tattaki zuwa majalisa, wanda shine na farko da aka yi hakan a tarihin Kaduna

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button