Labarai

Masha Allah : Kimanin Mutane Sama Sa Dubu 186 Suka Dawo Gida,Farin ciki Yasa Sun Fashe Da kukan Dadi( A Cikin Hotuna)

Advertisment

Al’ummar Garin Kukawa Dake Jihar Borno Sun Fashe Da Kukan Farin Ciki Bayan Sun Dawo Gida Bayan Sun Dauki Tsawon Lokaci Suna Gudun Hijira Sakamakon Rikicin Boko Haram

Kimanin mutane sama da dubu 186 suka dawo gida.

Daya daga cikin ‘yan gudun hijiran ya bayyana cewa “mun yi murna da dawo gida da muka yi ba wai don mun dawo da kudi a aljihunmu ba. Amma muna da yakinin cewa mun dawo don mu ci gaba da rayuwa a matsugunanmu.

Advertisment

“Shekaru goma da suka gabata na mallaki gonaki, motoci uku da rarar kudi sama da milyan shida da yara sha uku, amma yanzu yara bakwai ne suka rage min da kuma gona. Don haka ina mai godiya ga Allah da ya bar mu cikin rayayyu”.jaridar Rariya na kawo wannan labari.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button