Labari mai dadi : Tambuwal Ya Bada Umurni A Soma Biyan Kuddin Gratuity Ga Tsofaffin Ma’aikata Cikin Satinnan
Da yammachin yau lahadine Maigirma gwamna Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal CFR (Mutawallen Sokoto) ya umurchi ma’aikatar kudi data pensho da’asoma biyan kuddin qare aiki ga tsofaffin ma’aikata a jihar Sokoto.
Wannan yazone achikin wani meeting na gaggawa da’akayi yau dinnan tsakanin ma’aikatun guda biyu, cewa Maigirma gwamna ya bada umurni a soma biyan wayanna kudade, inda tuni Ma’aikatun sukayi amanna tare da alqawarin fara biyan kudin chikin wannan sati na watan August, 2020.
Bayan da dukkan shirye shirye sun kankama domin soma biyan wannan kudi na Gratuity, wayanda Suka fara barin aiki sune xa’afara biya harzuwa kammalawa… Haka kuma babu galihu babu banbanchin ko wariya da za’ayi amfani dashi alokachin wannan aiki.
![]() ![]() |
Kwamishinan kudi abdulsamad dasuki |
Idan Baku mantaba, shekaranjiya jumu’a ne akafidda sunayen sabbin ma’aikata dubu biyu (2000) da gwamnati ta dauka aiki anan jihar Sokoto, tareda soma muhimman ayukkan raya jiha wayanda Suka qunshi gadoji da tagwayen tituna.
yau lahadi kuma bisaga Umurnin Maigirma gwamna za’a fara biyan kudin Gratuity ga tsofaffin ma’aikatan gwamnati cikin wannan sati domin chigaba da gudanarda rayuwarsu.
Madogara: Unclè Anass Dukura.
Ahmad Kabeer.
Lahadi 23rd August, 2020