Kungiyar Izala Ta Yi Kira Ga Hukumar Tsara Jarabawar WAEC Da Ta Canja Lokutan Zana Jarabawar Da Ya Yi Daidai Da Lokutan Da Musulmai Ke Gudanar Da Ibada A Ranakun Juma’a
…Kazalika Kungiyar tana goyon bayan hukuncin kisa da wata kotu a Kano ta yankewa matashin da ya zagi Annabi S.A.W.
Daga Comr Abba Sani Pantami
Kungiyar Izala ta kasa karkashin jagorancin Sheikh Abdullahi Bala lau, tana kira ga Hukumar shirya Jarrabawar WAEC da ta chanja lokutan da ta sanya jarabawa a daidai lokacin da musulmai ke gabatar da sallar Jumma’a, wanda hakan kamar tauyewa musulmai hakkin su ne.
Hukumar shirya Jarabawar WAEC ta saka jadawalin zana jarabawa har guda ukku da suka ci karo da lokutan da musulmai ke gabatar da ibada ranar Jumma’a.
Jarabawar Farko: Jarabawar ‘Management-in-living’ wacce dalibai zasu zana a ranar Jumma’a 14 ga watan Augusta, 2020 da misalin karfe 2:00pm daidai.
Jarabawa Ta Biyu: Jarabawar ‘Literature-In-English’ wacce zasu zana ranar Jumma’a, 21 ga watan Augusta, 2020 da misalin karfe 2:00pm.
Jarabawa Ta Ukku: Jarabawar ‘Health Science’ wanda zasu zana a ranar 4 ga watan Satumba, 2020 da misalin karfe 1:30pm na Rana.
Haka zalika kungiyar tana jaddada goyon bayan ta ga hukuncin kisa da wata kotu ta yanke wa wani matashin da ya zagi Annabi S.A.W a jihar kano, wannan hukuncin shi ya dace da abunda ya aikata, da tuntuni ana yanke musu irin wannan hukuncin da an dade da samun saukin masu irin wannan batancin.