Uncategorized

Katin gayyatar ɗaurin auren Hanan Buhari da Turad Sha’aban ya fito (Hotuna)

Katin auren ‘yar autan Shugaba Muhammadu Buhari, Hanan da Turad Sha’aban ya fito.

Za a daura auren ne a ranar Juma’a 4 ga watan Satumbar shekarar 2020 misalin karfe 2 na rana.

Ana sa ran za a daura auren ne a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Wannan shine daurin aure na farko da za a daura a fadar shugaban kasar ta Aso Rock.

Angon dan tsohon dan majalisa ne, Alhaji Mahmud Sani Sha’aban da ya wakilci mazabar Zaria a Majalisar Wakilai ta Tarayya daga Mayun 2003 zuwa Mayun 2007.

Sha’aban kuma tsohon dan takarar gwamna ne a jihar Kaduna a karkashin tsohuwar jami’yyar Action Congress of Nigeria wato ACN.

Kazalika, Alhaji Mahmud Sani Sha’aban ne wakilin Tudun Wadan Zazzau.

Ba za ayi taro irin yadda aka saba ba na bikin aure duba da cewa har yanzu akwai annobar korona a kasar a cewar katin gayyatar hakan na nufin ba mutane da yawa za su hallarci daurin auren ba.

Ga dai katin gayyatan auren nan a kasa kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button