Kashi 40 na maza masu aure suna neman maza ƴan uwansu – Inji Jaruma Halima Abubakar
A kwanakin baya ne jarumar fina-finan kudancin Najeriya (Nollywood), Halima Abubakar, ta wallafa wani saƙo mai sarƙaƙƙiya a dandalin sada zumunta, Bayan ta wallafa saƙon ne masu bibiyar shafinta a dandalin sada zumunta sun roƙi jarumar ta fassara kalamanta domin su fahimci ma’anar dake cikin sa.
Jarumar ta wallafa cewa kar ku yi saurin zargin mutanen dake yawan neman mata wasu daga cikin su maza suke buƙata ba mata ba, Kar ka illata kan ka ka karkaɗe kurar jikinka ka ƙara gaba.
A wata tattanawarta da jaridar Punch a kan ma’anar saƙon da ta wallafa, jaruma Halima ƴar asalin jihar Kogi ta bayyana cewa kashi 40% na maza ma su aure a Najeriya suna neman maza a ɓoye, Muna da fiye da kashi 40% na maza masu aure a Najeriya da ke neman maza, ko zaka yadda ko ba zaka yadda ba, wannan magana haka take, babban abin haushin shi ne hatta iyalinsu basu san da hakan ba sun ɓoye mu su, suna jin tsoron bayyana musu, A haka ne suke sakawa matan su irin cututtukan da suka kwaso, ta ce Ni a nawa ganin zaifi kyau su fito fili su faɗi gaskiyar halinsu su saka buƙatun su a gaba fiye da komai.
Halima ta ƙara da cewar na san maza ma su aure da yawa da ke neman maza da mata ina faɗar hakan ne saboda gaskiya ne, masu irin halin ne suke ƙorafi akan magana ta, Me yasa namiji zai ta sauya mace haka kawai ya nemi wannan ya nemi waccan, me ya ke nema idan ba namiji ba? Mafi yawan ƴan Najeriya munafikai ne basa son karɓar gaskiya. Ni, Halima Abubakar na faɗa cewa akwai maza masu aure dake neman maza da mata, Su taimaki rayuwar na gaba ta hanyar bayyana halinsu idan kuma ba zasu iya ba, su haƙura da aure kawai a cewar jarumar.
Sannan ta ci gaba da cewa idan kuma haihuwa ce basa buƙata kawai za su iya daukan raino, abun haushin wasu daga cikin su ma suna da yara da yawa amma duk da haka suke neman maza, na daɗe ina ankarar da jama’a hakan yanzu ne lokacin da zan yi magana irin wannan ya zo. Jarumar ta yi watsi da masu zargin cewa ta na yiwa tsohuwar kawarta, Tonto Dikeh, shaguɓe ne kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai ke yaɗawa.