Labarai

KANO: An Zartar da Hukuncin Kisa Kan Wanda Ya Yiwa Annabi Batanci

Wata kotu dake filin Hockey a Unguwar Hausawa dake jihar Kano, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya akan wani matashi dan shekaru 22 sakamakon samun sa da laifin yiwa fiyayyan halitta Annabi Muhammadu batanci.

Majiyar shafin Madubi-H ta ruwaito cewar, Alkalin kotun  Khadi Aliyu Muhammad Kani, shi ya yanke hukuncin a yau Litinin bayan sauraren shaidu daga kowane bangare, daga karshe an samu Yahaya Aminu Sharif da laifin yiwa Annabi batanci a wata wakar da ya rera.

Sharif, wanda yake unguwar Sharifai a cikin birnin Kano, an kama shi ne a watan Mayun shekarar 2020 yayinda ya rera wakar batanci ga Annabi Muhammadu, wanda sanadiyar wakar aka samu hatsaniyar da ta kai ga wasu mafusata suka rushe gidan iyayensa.

Daga MADUBI-H

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button