Addini

Kadan Daga Darajojin Annabi SAW (40) ( littafin Hadayatul sul ila tafdilil Rasul) ~Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kano

Advertisment

Manzon Allah saw yace : Ɗayanku bashi da imani har sai yafi sona fiye da yadda yake son ƴaƴansa da iyayansa, da dukkan mutane baki ɗaya.
Muna son Annabi saw, saboda :

1       SHINE SHUGABANNI YAN ADAM BAKI ƊAYA..
2       SHINE MAI TUTAR YABO RANAR ALKIYAMA .
3       SHINE WANDA  TUN DAGA ANNABI ADAM SAW, HAR ZUWA ƘASA SUNA  KARKASHIN TUTAR SA RANAR KIYAMA.
4      SHINE FARKON MAI NEMAN CETO.
5      SHINE FARKON WANDA ZAA BAWA CETO.
6      SHINE AKA YAFE MASA ABINDA YA WUCE DA ABINDA ZAIZO  ( IDAN MA YAYI)
7      SHINE ALLAH YAYI RANTSUWA DA RAYUWAR SA.

8      SHINE WANDA ALLAH TA’ALA BAYA KIRANSA DA SUNAN KAI TSAYE, (SAW)  ,  SAI YA ANNABI     YA MANZO  YA  MAI LULLUBA.
9      SHINE WANDA YA JINKIRTA ADDUAR SA TA ZAMA CETO GA AL’UMMAN SA RANAR ALKIYAMA.

10    SHINE WANDA DUTSE YAKE YI MASA SALLAMA.
11    SHINE  WANDA KUTUTTURAN DABINO YAYI KUKA SABODA RABUWA DA SHI.
12    SHINE WANDA RUWA YA FITO TA TSAKANIN HANNUNSA.
13    SHINE  WANDA AKA CIREWA  WANI SAHABI IDO A  WAJAN  YAKI YA MAYAR MASA NAN TAKE. KUMA YA WARKE NAN TAKE .
14     SHINE WANDA YAFI KOWA KYAWUN HALITTA.
15     SHINE WANDA YA FADI KOWA KYAWUN HALI.
16     SHINE WANDA ZAA DOSA RANAR ALKIYAMA, BAYA ANJE WAJAN KO WANNE ANNABI, YA BADA UZRI.
17     SHINE AKA AIKO GA DUK DUNIYA, AMMA SAURAN ANNABAWA GA AL’UMMAR SU KAWAI.

Advertisment

18    SHINE  WANDA  ƘASA ZATA FARA TSAGEWA YA FITO RANAR ALKIYAMA.
19    SHINE   MAI WASEELA DA FADEELA. (MANYAN DARAJOJI)
20    SHINE MAI TAFKIN KAUSARA.
21     SHINE WANDA ZAI FARA  SHIGA ALJANNAH DA AL’UMMAR SA.
22     SHINE WANDA MUTUM DUBU 70 ZASU SHIGA ALJANNAH BABU HISABI DAGA AL’UMMAR SA.
23     SHINE  LITTAFIN SA YAFI DUKKAN LITTAFIN DA AKA SAUKAR.
24     SHINE WANDA AKA HALASTAWA AL’UMMAR SA GANIMA BAYAN TA HARAMTA GA WADANDA SUKA GABATA.
25      SHINE WANDA AKA HALASTAWA AL’UMMAR SA SUYI TAIMAMA DA ƘASA.
26      SHINE WANDA AKA SANYAWA AL’UMMAR SA KO’INA YA ZAMA MASALLACI IN BANDA MAQABARTA DA BANƊAKAI. (ZA SU IYA SALLAH A KO’INA.)

27      SHINE WANDA AL’UMMAR SA TAZO A KASHE, AMMA TAFI WADANDA SUKA GABATA DARAJA.
28      SHINE WANDA YAYI ISRA’I DA MI’IRAJI HAR SUKA YI MAGANA DA ALLAH TAALA,  HAR YA KARBO SALLAH.
29      SHINE   WANDA YAFI ANNABAWA YAWAN MABIYA DA YAWAN LADA.
30      SHINE WANDA AKA NINKAWA AL’UMMAR SA  AIKIN LADA DAYA, ZUWA GOMA.
31     SHINE  MU’UJIZAR SA BATA YANKEWA DA WUCEWARSA.
32      SHINE WANDA DUK YA BISHI ZAI SHIGA ALJANNAH WANDA YA SABA MASA BAYA SO.
33      SHINE WANDA IDAN KAYI MASA SALATI DAYA, ALLAH ZAIYI MAKA GOMA.
34       SHINE  WANDA ALLAH YA SANYA MAKULLAN TASKOKIN ƘASA A HANNUNSA.
35        SHINE  WANDA YAFI KOWA SAN ALLAH, KUMA ALLAH YAFI SON SA.
36        SHINE WANDA SAI KAFI SON SA, FIYE DA IYAYANKA, DA YA’YANKA, DA KANKA, DA DUK DUNIYA BAKI DAYA, SANNAN ZAKA TABBATA MAI IMANI.

37       SHINE WANDA IDAN KAYI MASA SALLAMA, ALLAH YAKE DAWO MASA DA RANSA YA AMSA MAKA SALLAMAR KA.
38        SHINE WANDA AKA SIFFANTA AL’UMMAR SA DA ADALCI DA SHEDAR DA ZASU YIWA ANNABAWA, AKAN SUN ISAR DA SAKO.
39        SHINE  WANDA AL’UMMAR SA BATA HADUWA AKAN BATA.
40        SHINE SAHIBUL MAKAMIL MAHMUD SAW.
ALLAH YA KARA MANA SON ANNABI DA BIYAYYA A GARESHI.
ALLAH TSINEWA MASU TABA DARAJAR ANNABI SAW.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button