Labarai
INDA RANKA: Ya Kori ‘Yarsa ‘Yar Shekara Takwas Daga Gidansa Saboda Idonta Ya Yi Kama Da Na Kyanwa
Daga:jaridar rariya a Facebook na ruwaito.
- Wani Magidanci a garin Ilori dake jahar Kwara ya kori diyarsa ‘yar shekara takwas a gida bayan an haifa mai ita da idaniya irin na mage.
Magidancin yace ba zai iya rayuwa da diyar ta sa ba saboda tana ba shi tsoro idan dare ya yi musamman idan yana kallo idanunta.
Ya ce babban abunda ke ƙara ba shi mamaki da yarinyar shine yadda idaniyanta ke haske tamkar na mage idan ka haska mata fitila idan dare ya yi, wanda ya ce duk lokacin da ya dubi diyar tasa ba ya ƙara marmarin kallon ta saboda idaniyanta na tsorata shi a koda yaushe wanda hakan ya sa dole ya ce ta bar masa gidansa domin ya samu rayuwa cikin salama.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com