Labarai
Iftila’in Beirut: ‘Abin da muka sani kawo yanzu
Advertisment
Masu aikin ceto a Lebanon na can suna kwashe ɓaraguzan gine-gine domin ceto waɗanda suka tsira daga iftila’in fashewar wasu sinadarai da aka jibge cikin tashar jirgin ruwan Beirut ranar Talata da ya kashe mutum 137 kuma ya jikkata fiye da mutum 5,000.
Ga abin da muka gano kawo yanzu.
Mene ne ya faru?
Fashewar ta haifar da wata gagarumar gobara a tashar jirgin ruwan Beirut, wadda ke gabar tekun Bahar Rum. Cikin hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta, ana iya ganin farin hayaƙi na tashi daga wani ɗakin ajiyar kaya mai lamba 12 wanda ke daura da wani katafaren rumbun adana hatsi.
Jim kaɗan bayan ƙarfe shida na yamma, rufin ɗakin ajiyar kayan ya kama da wuta kuma an ji fashewar wani abu na farko, daga baya kuma an riƙa jin ƙarar fashewa masu dama da suka yi kama da wutar nan da ake wasa da ita lokacin bukukuwa.
Bayan kimanin daƙiƙa 30, sai wani ƙara mai gigitarwa ya ratsa birnin kuma ya fitar da wani farin hayaƙi wanda ya turnuƙe samaniya.
Advertisment
Hucin fashewar da ya biyo ƙarar ya ruguza dukkan gine-ginen da ke kusa da tashar jirgin ruwan kuma ya yi mummunan ta’adi a sauran unguwannin birnin mai mutum miliyan biyu. Nan take asibitoci suka cika da marasa lafiya har ta kai lamarin ya sha ƙarfinsu.
“Abin da muke shaidawa katafaren iftil’ai ne,” inji George Kettani shugaban ƙungiyar Red Cross. “Akwai waɗanda bala’in ya rutsa da su ko’ina.”
Gwamnan Beirut Marwan Abboud ya ce kusan mutum 300,000 sun rasa muhallansu kuma asarar da aka yi a birnin na iya kai wa tsakanin dala biliyan 10 zuwa biliyan 15.
Yaya girman fashewar ya ke?
Kwararru ba su auna karfin fashewar kawo yanzu ba, amma hucin fashewar ya tarwatsa tagogin filin jirgin saman Beirut na ƙasa da ƙasa wanda ke da nisan kilomita 9 daga tashar jirgin ruwan.
An kuma ji ƙarar fashewar a ƙasar Cyprus mai nisan kilomita 200 daga wurin – wanda kuma ke cikin tekun Bahar Rum ne. Cibiyar da ke auna ƙarfin girgizar ƙasa ta Amurka ta United States Geological Survey ta ce ƙarfin fashewar dai-dai yake da girgizar ƙasa da ta kai maki 3.3.
Mene ne sanadin fashewar?
Shugaban Lebanon Michel Aoun ya ɗora alhakin fashewar tan 2,750 na sinadarin ammonium nitrate da aka jibge cikin wani ɗakin ajiyar kaya na tashar jirgin ruwan birnin.
A shekarar 2013, wani jirgin ruwa mai suna MV Rhosus yayi jigilar sinadarin. Bayan ya yada zango a tashar jirgin ruwa na Beirut saboda wata matsalar inji a kan hanyarsa daga ƙasar Georgia zuwa Mozambique, sai hukumomin tashar suka hana shi barin tashar bayan sun binciki kayan da yake ɗauke da su.
Kamar yadda shafin intanet na Shiparrested.com ya ruwaito, masu jirgin ruwan sun yi watsi da lamarin jirgin ruwan nasu a tashar, lamarin da yasa aka kwashe sinadarin daga ciki zuwa wani ɗakin ajiya mai lamba 12 bayan wata kotu ta bayar da umarnin yin haka.
Tun wancan lokacin sinadarin ke jibge cikin ɗakin, maimakon a sayar da shi ko dai a raba shi da wurin.
Masana na cewa ana iya adana ammonium nitrate ba tare da matsala ba idan aka kiyaye wasu sharudda. Amma idan ya yi yawa kuma ya daɗe a ajiye, ya kan fara ruɓewa.
A shekarun baya sinadarin na ammonium nitrate ya janyo manyan hadurra. A 1947, wani jirgin ruwa ɗauke da tan 2,000 na sinadarin ya fashe a jihar Texas ta Amurka inda ya kashe mutum 581.
Kan wa alhakin wannan bala’in ya ke?
Shugaba Aoun ya yi alƙawarin gudanar da cikakken bincike kan fashewar.
“Mun ƙuduri niyyar ci gaba da bincike kuma za mu bayyana yadda wannan abin takaicin ya auku ba tare da jinkiri ba, kuma duk wadanda aka samu da sakaci da ya janyo fashewar za su ɗandana kuɗarsu,” inji shugaban ranar Laraba bayan ya zaga cikin tashar jirgin ruwan.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com