Hira Da Limamin Wuff : Yadda Limamin Wuff Ya Bayyanawa Yan Jaridar Akan Rabuwar Aurensa Da Hajiya Balkisu
A safiyar ranar Litinin dinnan ne wato 10-08-2020 kafar sada zumunta ta kasance da ce-ce-kucen jama’a tare da rade-radin mutuwar auren fitaccen jarumin fim din masana’antar Kannywood, Abdulaziz Shuaibu wanda a ka fi sani da Mallam Ali na cikin fim din nan mai dogon zango na Kawan Casa’in na tashar Arewa24, cewa sabon auren da ya yi a kwanakin baya da zukekiyar Amaryar sa Hajiya Bilkisu Shibah ya mutu.
Kimanin watanni biyar da su ka shude hotunan jarumin tare da Hajiya Shibah su ka dauki hankalin dandalin soshiyal midiya, wanda ta kai mutane na tofa albarkacin bakin su dangane da yawan shekarun da ta ba shi da kuma ganin jarumin bai haura shekara guda da auren tsaleliyar matashiyar matar sa ta farko ba.
Ko da ya ke, dai mutane na zargin dukiyar Hajiya Shibah ce ta rudi jarumin har ya kai ga auren ta, amma jarumin ya fito ya bayyana dalilan sa na auren Sahibar Amaryar sa Hajaju da ya yi, wanda ya ba da hujja da ko yi ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
To sai dai kwatsam a daren jiya sai ga wannan jita-jita na yawo a kan mutuwar auren na Abdulaziz da Hajiya shiba, amma da ya ke ba ma Kwan mu sai da Zakara kamar yadda ma su magana ke cewa, abun da ya sa wakilin mu ya tuntubi Ango kamshi sha guda, domin jin sahihancin wannan labari, ga kuma yadda hirar ta su ta kasance.
To da farko Malam Ali ga wannan ce-ce-kuce da ya dauki hankalin jama’a a shafukan sada zumunta, ko me za ka iya cewa a kan rabuwar auren na ku da Amaryar ka Hajiya Bilkisu, tun da dai an ce magana a bakin me ita tafi dadi?
“To ni ma dai haka na ke ta ji a na fada a dandalin soshiyal midiya wai cewa mun rabu da Amarya ta”.
Hakan na nufin ba gaskiya ba ne ba labarin rabuwar auren na ku, ko ma iya cewa labarin kanzon Kurege ne?
“To gaskiya ba zan ce komai ba a yanzu har sai nan da wani lokaci tukun na, sai na bayyana gaskiyar abun da ya ke a kasa”.
To amma wani abu da mutane ke gani, har sun ta yin rade-radin mutuwar auren ku, ko kun dan samu sabani ne har labarin ya fita ba tare da son a ji kanku ba, tun da mutane na ganin dama auren na ku kamar ba zai dade ba?
“Kamar dai yadda na fada maka a baya, zan fadawa duniya duk abun da ya ke a kasa, amma ba yanzu ba”. Inji Abdulaziz.
To wannan dai shi ne abun da jarumi Abdulaziz ya tabbatar mana cewa ba za a ji komai daga bakin sa ba dangane da mutuwar auren da a ke ta yamadidi a kai. Za kuma mu bibiyi labarin domin turewa Buzu nadi ko kuma mu ce mu ji yadda a ka haihu a Ragaya.
Idan mai karatu bai manta ba, a baya dai sai da wannan aure na jarumi Malam Ali ya zama abun kwatance a shafukan sada zumunta da kuma kafar rediyo, musamman ma wata sabuwar kalma da a ka rinka amfani da ita wai cewa Malam Ali ya yi wuf da sabuwar Amarya.northflix na wallafa.