DA DUMI DUMINSA: Gwamnatin Buhari Ta Dawo Da Tallafin Man Fetur A Nijeriya
Sababbin alkaluman da kamfanin NNPC ya fitar ta nuna cewa gwamnati ta fitar da Naira biliyan biyar domin cike gibi a watan Yunin shekarar nan.
Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa NNPC ta biya makudan kudi a sakamakon banbamcin da aka samu wajen saida man fetur a gidajen mai ta yadda za a ci riba.
Abin da gwamnatin tarayya ta biya ta hannun NNPC shi ne Naira biliyan 5.348bn, ta hakane masu harkar mai za su ci riba a kan yadda su ka rika saida lita.
A cikin watan Maris, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dakatar da biyan tallafin man fetur. Wannan ya sa litar man fetur ya kara tsada a Najeriya.
An shafe kusan watanni uku ma’aikatar PPPRA ta na tsaida kudin man fetur ne a kowane wata tare da la’akari da yadda farashin gangar mai ya ke a kasuwar Duniya.
Bayanan da NNPC ta fitar na watan Yunin 2020, ya nuna an cirewa ‘yan kasuwa asara da biyansu Naira biliyan 5.348 da aka yi a wannan lokaci inji jaridar kasar.
NNPC ne ya ke shigo da mafi yawan tataccen man fetur a Najeriya. A watan Maris, rahotanni sun nuna kamfanin gwamnatin tarayyar ne kadai ya rika jigilar mai. Shafin rariya na ruwaito.