Bidiyo: Innalillahi wa’innah alaiihi Raju’un Subhanilillahi :Matar Ubansa Ta Kullesa A Daki Shekara Bakwai
ME WASU MATAN SU KA DAUKI KISHI NE?
Tabbas na san kishi bai da dadi, amma bai kai abun da mace za ta bari ya zama hanyar shigarta wuta ba, kar kishi ya rufe mana ido mu haukace mu makance, mu zama azzalumai, mata da tausayi aka sammu amma wasu abun da su ke aikata ko mara imani ba zai aikata ba wai da sunan kishi kaico, yanzu aka turo min wannan rubutun da Bidiyon na kasa, mu ji tsoron Allah, mu rage zazzafan kishi, duniyar nan fa za mu barta ko muna so ko ba ma si.
Wannan bawan Allah da kuke gani a bidiyon nan dake kasa, Matar ubansa ce ta kulleshi a daki shekara bakwai ba ci ba sha, sai dai yaci kashinsa da fitsarinsa..
A unguwar Mariri dake nan jihar mu mqi albarka ta Kano, shine jiya Rahma suka cetoshi..
A jiyan har zuwa goma na dare su Rahma suna police station na unguwar Farawa.
Ga Bidiyon nan zaku iya kallo.