Labarai

BATANCI GA MA’AIKI: Kira Na Musamman Ga Gwamnatin Jihar Kano – Daga Indabawa Aliyu Imam

Mun kira ga gwamnatin jihar Kano da ta tsaya kai da fata wajen bi wa Manzon Allah S.A.W hakkinsa da wani la’ananne ya taba a garin Kano, an ce amincewar gwamnatin kadai ake jira a zartar da wannan hukunci, sai dai kawo yanzu ba mu ji komai daga gwamnatin ba.

Tabbas idan har aka bari wannan lamari ya tashi a banza kamar yadda ya faru a baya, hakan na iya harzuka mutane su tashi su dauki mataki da kansu.

Tabbatar da wannan hukunci shi zai karawa wannan gwamnati ‘kima da daraja a idanun musulman duniya, kuma zasu bada shaida a gaban Allah cewa sun kiyaye hakkin manzonsa da yake rataye a wuyansa.

Zartar da wannan hukunci zai kara fito da kima da daraja ta shugabanmu Masoyinmu S.A.W ga makiyansa, kuma hakan zai zama darasi ga mutane.

Allah ya kara mana soyayyar Manzon Allah S.A.W.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button