Labarai
Bankin Musulunci TAJ BANK Ya Bude Sabon Reshen Shi Na Uku A Nijeriya A Jihar Sokoto (Hotuna)
A yau Litinin Mai Girma Gwamnan jihar Sokoto R.t Amin Waziri Tambuwa ya kaddamar da bikin bude sabon bankin musulunci mai suna TAJ BANK a jihar Sokoto, wanda yake shine na uku a Nijeriya bayan wanda yake a Kano da Abuja.
Shi dai wannan banki na TAJ BANK an kirkiro shi ne a shekara ta 2019, kuma shine banki na biyu na musulunci a Nijeriya bayan JAIZ BANK, kuma su ne bankuna da ba su karbar kudin ruwa.
Allah ka daukaka wadannan bankuna, ka sanya albarka a tare da su.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com