Labarai

ALHAMDULILLAHI: Yanzu Yaro Isma’il Ya Zama Cikakken Dan Kasuwa Bayan An Bude Masa Katafaren Shago Sakamakon Yadawa Duniya Labarinsa Da RARIYA Ta Yi (Hotuna)

Advertisment

Daga Aliyu El-Idrith Shu’aibu (Dan Autan Media)

Kamar yadda RARIYA ta yi alkawari a yau Asabar za ta tattara bayanan irin tallafin da yaron ya samu daga wuraren al’umma domin jama’a su san cewa sakon su ya isa gare shi, Alhamdulillah an samu damar budewa yaron katafaren shago a kofar gidansu.

Idan ba a manta ba dai, a ranar Lahadin da ta gabata ne RARIYA ta sanya hoton Ismail dan asalin karamar hukumar Rano dake Kano ya zuba magi kwara shida da onga kwara biyu a cikin kwali yana sayarwa a kofar gida. Wanda tunda daga wannan lokacin ne jama’a suka bukaci RARIYA da ta binciko adireshin yaron domin tallafa masa da jari. Inda RARIYA ba ta yi kasa a gwiwa ba ta tura wakilinta ya je har garin su yaron domin tabbatar sahihancin sana’ar tasa.

Cikin ikon Allah jama’a da dama da kungiyoyi daban-daban daga sassan kasar nan sun ba shi gudummawa kama daga ta kudi, kayan shago, inda kuma aka samu wanda ya dauki nauyin karatun sa tun daga matakin firamare har zuwa jami’a tare kuma da ba shi aiki da zarar ya kammala karatu.

A madadin Yaro Isma’il da mahaifansa, RARIYA ta na godiya ga dukkan wadanda suka ba shi gudummawa da ma wadanda suka yi masa fatan alheri.

Ga hotunan na shagon wannan yaron dan kasuwa rano

Gaban shagon isma’el Rano kenan bayan samun cigabansa

Farkon fara sana’ar Isma’el Rano
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button